1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake kafa dokar ta baci a Sri Lanka

Abdul-raheem Hassan MAB
July 18, 2022

Gwamnatin Sri Lanka ta kafa dokar ta ba ci don kawar da shirin haddasa rikici gabannin zaben sabon shugaban kasa a majalisar dokoki a karshen wannan mako.

https://p.dw.com/p/4EGWV
Sri Lanka's Prime Minister Ranil Wickremesinghe
Firaiministan Sri Lanka kuma Shugaban rikon kwarya Ranil WickremesingheHoto: Adnan Abidi/REUTERS

Rahotanni daga Colombo babban binrin kasar Sri Lanka na cewa an wayi gari shuru da takaita zirga-zirga a kan titunan birnin.  Tun dai a watan Afirilu, tsohon Shugaban kasar Sri Lanka da ya tsere bayan da 'yan kasar suka mamaye fadarsa, ke sanya dokar ta baci don rage tasirin zanga-zangar yin tir da gwamnatinsa kan tsadar rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki.

A ranar Asabar mai zuwa ne majalisar dokokin kasar Sri Lanka za ta gana don fara aikin zaben sabon shugaban kasa, Sri Lanka dai ta roki asusun bada lamuni na duniya da ya samar da agajin gaggawa, amma rudanin siyasa ya kawo tsaiko a tattaunawar.