1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Sri Lanka na neman IMF ya tallafa mata

March 17, 2022

Shugaban kasar ya ce ya fara magana da sauran hukumomin duniya kan yiwuwar kasar ta tsagaita biyan basussukan da ake bin ta domin a yanzu kasarsu na cikin masassarar tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/48bXW
Sri Lanka | Wahlen | Päsident Gotabaya Rajapaksa
Hoto: AFP/I.S. Kodikara

Kasar Sri Lanka za ta nemi tallafin kudi daga Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF. Shugaban kasar Gotabaya Rajapaksa ne ya sanar da haka a wani jawabi da ya yi wa kasar bayan wata gagarumar zanga-zangar da aka yi wa gwamnatinsa kan ci gaba da durkushewa da tattalin arzikin kasar ke yi. Ya kuma bukaci 'yan kasar su tallafa ta hanyar rage amfani da wutar lantarki da man fetur.


Sri Lanka da ke nahiyar Asiya dai ta kwashe makonni tana shaida yawaitar tashin farashin kayan abinci babu kakkautawa, ga kuma karancin man fetur da ya dabaibaye kasar.