Steinmeier na iya zama shugaban Jamus
November 14, 2016A ranar Litinin din nan ce jam'iyyu da ke kawance da jam'iyyar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel suka amince da zabin ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier don ya zama dan takarar shugabancin kasar a zaben da ke tafe shekara mai zuwa. Wannan dai na nufin sai an sake kwaskwarima a majalisar zartarwar kasar ta Jamus.
Kawancen Jam'iyyun da CSU sun amince da zabin na Steinmeier don kaucewa gwama numfashi da jam'iyyarsa ta SPD a kokarinsu na ganin damar ba ta kwace wa aminansu da ke cikin kawancen gwamnati ba.
Shugaban jam'iyyar ta SPD Sigmar Gabriel ya ce lokaci ya yi wuri a fara batun wanda zai maye gurbin Steinmeier a matsayin ministan harkokin kasashen waje. A watan Fabrariru ne dai za a yi zaben shugaban kasar wanda Steinmeier ke fatan zama shugaban na Jamus inda zai maye gurbin Shugaban kasar mai barin gado Joachim Gauck.