Su waye manyan 'yan takara a zaben Jamus na 2025?
Gabannin babban zaben Jamus da ke tafe a watan Fabarairu, jam'iyyun siyasar kasar sun tsayar da 'yan takarar su.
Olaf Scholz, jam'iyyar SPD (An haife shi a shekarar 1958)
Dan jam'iyyar Social Democrats wanda ke da kamfanin lauyoyi, ya shafe shekaru ana gwagwarmayar siyasar Jamus da shi, ya rike mukaman gwamnati kama daga magajin garin birnin Hamburg da ministan kwadago da ministan kudi da ma shugaban gwamnati. Olaf Scholz ya kasa daukaka kimarsa ta yadda zai kara samun kwajini a tsakanin al'umma.
Friedrich Merz, jam'iyyar CDU (An haife shi a sheklarar 1955)
Mai ra'ayin yan mazan jiya, Friedrich Merz dan takarar neman kujerar shugaban gwamnati mafi tsufa da Jamus ke gani a sama da shekaru 50, Merz Lawyan dan kasuwa ne kuma mai bin darikar Katolika da ya fito daga yankin yammacin Jamus bai taba rike mukamin gwamnati ba, sai dai yana da gogewa a fannin kasuwanci tare da kasancewa daya daga cikin manyan kamfanonin kadarori na duniya BlackRock.
Robert Habeck, jam'iyyar Greens (An haife shi a shekarar 1969)
Robert Habeck da ake wa kallon mai saukin kai, dan siyasar da ba shi da matsala wajen amsa kuskurensa, Habeck ne ya samo kalamai masu sauki da ratsa zuciya don bayyana hukunce-hukuncen siyasa na gwamnati ga jama'a tare da kawar da girman kan abokan kawancensa. Kafin shigar sa siyasa, Habeck marubuci ne, mai fassara kuma masanin falsafa.
Alice Weidel, jam'iyyar AfD (An haife ta a shekarar 1979)
Alice Weidel mataimakiyar shugaban jam'iyyar masu kyamar baki, mai ra'ayin 'yan mazan jiya tana da digirin digirgir a fannin tattalin arziki, ta yi karatu da aiki a kasar China. Weidel na da tsatsauran ra'ayi a kan bakin haure. Yanzu haka tana rayuwa da wata mace kawarta 'yar asalin Sri Lanka a kasar Switzerland inda suke da 'ya'yan riko biyu.
Christian Lindner, Jam'iyyar FDP (An haife shi a shekarar 1979)
Tsohon ministan kudi wanda masanin kimiyar siyasa ne, Christain Lindner ya samar da kamfanin yin sana'ar talla kazalika jami'in sojin ajiya ne a rundunar sojin saman Jamus. Ya zama shugaban jam'iyyarsa ta Free Democrats tun yana da shekaru 34 kacal kuma ya ci gaba da zama shugaba ba tare da wata hammaya ba. Lindner ya lakanci kafofin sadarwar zamani kuma yana matukar sha'awar motocin wasanni.
Sahra Wagenknecht, jam'iyyar BSW (An haife ta a shekarar 1969)
Sahra Wagenknecht jigo ce a jam'iyyar 'yan gaba dai gaba dai, tana yawan ziyarar shirye-shiryen siyasa a kafofin talabijin. Ta yi suna wajen yi wa 'yan siyasa dariya da ma kiransu masu fuska biyu musamman masu ra'ayin mazan jiya da masu kyamar baki. Wagenknecht na da shakka a kan sauyin yanayi da ma sukar kungiyar tsaro ta NATO.
Jan van Aken, jam'iyyar yan gaba dai-gaba dai (An haife shi a shekarar 1961)
Jan van Aken haifafen Jamus Ta Yamma, yana da digirin digirgir a fannin ilimin halitta, ya kuma yi aiki a matsayin mai binciken makamai a Majalisar Dinkin Duniya. Ya yi zaman majalisa daga jam'iyyar 'yan gaba dai-gaba dai a majalisar dokoki ta Bundestag daga shekarar 2009 zuwa 2017. Tun a watan Oktoban 2024 ya kasance mataimakin shugaban jam'iyyarsa.