Sudan: Binciken MDD a kan kisan kare dangi
August 11, 2023Jagoran tawagar farko, Marta Reudas,wacce ta ganewa idonta kufayin kauyukan da aka kone ,ta kuma zagaya wasu daga cikin sansanonin da ake jinyar masu raunuka,ta ce, tagwar za ta raba kayayyakin abinci da ya kai tan 430, tana mai kira ga bangarorin da ke fada da su yi wa Allah da Annabi su dakatar da yakin. "Sudan dama a gaskiya ta jima tana fama da matsalolin rikice-rikice ba.Wannan yakin da ya barke tun kusan watanni hudu ya kara tada tsohon miki ne. A kwai bukatar duniya ta kara matsa lamba don ganin an kawo karshen wannan yakin. A kuma kara matsa kaimi wajen agazawa,domin taimako da ake dashi a yanzu bai kai yawan bukatar da ake da ita a kasa ba.”
An karkashe mutane da yawa mata yara da tsofi a yankin
Mahjoub Uthman,mukaddashin gwamnan jjihar Niyalah, yayi wa tawagar ta MDD bayani kan irin mawuyacin halin da mazauna sansanin Zam-Zam ke ciki: "Wallahi mutane a wannan sansanin tun kwanaki biyu ba mu samun abun da za mu ba su su kai bakin salati ba.Galibinsu kamar yadda kuke gani mata ne da yara kanana da tsofi.An kakkashe mazajensu ,wasu kuma an tarwatsasu.”
Wakilan MMD a Gabashin Darfur na gudanar da bincike
Wasu daga cikin wadanda suka tsira da ransu daga hare-haren da suka kira na kisan kiyashi da mayakan dakarun RSF da 'yan Janjaweed suka kai musu,sun bayyana irin tashin hankalin da suka gamu da shi wakilin binciken neman sanin gaskiya na MDD,William Deoun: "Motocin yaki masu dauke da rokoki na rundunar RSF ne suka yi ta lugudan wuta kan garinmu sai da suka kone shi kurmus.An kasha fiye da magidanta 500. A garin namu akwai fiye da mutane dubu 20.Yanzu babu kowa a cikinsa ya zama kufai,bayan da suka koneshi kurmus. Mu don muna da sauran shan ruwa a duniya ne, muka yi sa,ma muka tsere,bayan da muka baro masu raunuka da gawwakin 'yan uwa a warwatse kan hanya.”Bayan kaddamar da agajin gaggawa,da kimanta bukatar da ake da ita ta kudaden dauki, tawagar da za ta kwashe mako guda tana zagaya yankin na Darfur, karkashin tsauraran matakan tsaro na dakarun MDD, za ta tattara bayanai da shaidu kan zarge-zargen kisan kiyashi da fyade da aka yi wa mata kan dalilai na nuna wariya da kabilanci,don gabatar da bsu ga kwamatin tsaro na MDD,da zai tantance matakan doka da ya wajaba a dauka kan wadanda suka tafka wannan aika-aikar.