Fada tsakanin sojoji a Sudan
April 16, 2023Talla
An sha artabun tsakanin dakarun gwamnati da na wata rundunar sojojin sa kai da ke taimaka wa dakarun gwamnati wato RSF. Rundunar wacce ke kunshe da dubban tsaffin mayakan sa-kai na yakin Darfur, ta ce tana rike da gidan shugaban kasa, tare da karbe iko da filin saukar jirgin saman birnin Khartum da sauran muhimman wurare. Sai dai gwamnatin ta musunta haka,amma ta yarda cewar rundunar ta kona jiragen sama a ciki har da na kamfanin jiragen sama na Saudi Arabia. Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga bangarorin biyu wato shugaba Abdel Fattah al-Burhane da kuma jagoran rundunar ta RSF Mohamed Hamdane Daglo da su kai zuciya nesa.