Mako na uku da barkewar rikicin Sudan
May 5, 2023Masu aiko da rohotanni sun ce a yayin da ake cika mako na uku da barkewar rikicin bangaron biyu sun yi ta barin wuta a wasu unguwanni na birnin Khartum da kuma kusa da filin sauka da tashin jiragen sama, duk da alkawarin da suka dauka na mutumta sabuwar yerjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma har da wa'adinta zai kare a ranar 11 ga wannan wata na Mayu da muke ciki. Sai dai a ci gaba da rarrashin bangarorin biyu da kasashen duniya ke yi gwamnatin Masar ta ce ta tattauna ta waya da manyan hafsoshin sojan biyu, sannan kuma ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa za su yi zama na musanman kan batun. A daya hunnun kuma sojojin da ke biyayya ga Janar Abdel Fattah al-Burhane sun sanar da nadin manzon da zai wakilce su a zaman sulhun da ake sa ran yi karkashi jagorancin shugabannin kasashen Sudan ta Kudu da Kenya da kuma Jibuti, sai dai har kawo yanzu ba a sanar da inda za a gudar da zaman ba.