1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta yi farin ciki da dage takunkumin Amirka da ke kanta

Gazali Abdou Tasawa MNA
October 7, 2017

Amirka ta janye takunkumin tattalin arzikin da ta kakaba wa Sudan shekaru 20 da suka gabata.

https://p.dw.com/p/2lQH4
Sudanesischer Präsident Omar al-Baschir
Shugaba Omar al-Bashir na SudanHoto: Ashraf Shazly/AFP/Getty Images

Gwamnatin Amirka ta sanar a ranarJumma'a da dage wa kasar Sudan takunkumin karya tattalin arzikin da ta kargama mata shekaru 20 da suka gabata. Gwamnatin Shugaba Donald Trump ta ce ta dauki wannan mataki ne ta la'akari da kokarin da kasar ta Sudan ta yi wajen bayar da hadin kanta ga kasar ta Amirka a watanni tara na baya bayan nan.

Tuni dai gwamnatin kasar ta Sudan ta bayyana farin cikinta da wannan mataki da Amirka ta dauka a yanzu wanda ke zama daya daga cikin 'yan kwarorin manufofin tsohuwar gwamnatin Shugaba Obama da gwamnatin Trump ta amince ta ci gaba da aiwatar da su.

Daga nata bangare gwamnatin kasar ta Sudan ta daukar wa kasar ta Amirka wasu alkawurra biyar da suka hada da dakatar da bayar da tallafi ga kungiyoyin 'yan tawayen Sudan ta Kudu da kai hare-hare a yankin Darfur da na Kudancin Kordofan da kuma hada kai da hukumomin leken asirin Amirka cikin aikin yaki da ta'addanci.