Rikicin siyasar Sudan na neman korar Kasashen Yamma
November 21, 2022Cikin 'yan makonnin da suka gabata, masu zanga-zanga a Sudan sun yi ta sukar manufofi masu nasaba da kasashen ketare da kakkausar lafazi.
Guda daga cikin boren dai shi ne na neman a dauke jakadan Jamus Volker Perthes daga kasar, jami'in kuma da ke jagorantar shirin Majalisar Dinkin Duniya na sake dawo da kasar bisa doron dimukuradiyya.
Jakadan na Jamus wanda ya ce ba ya jin dadin yadda 'yan kasar ta Sudan ke dora laifin abubuwan da ke faruwa cikin kasarsu a kan wasu mutane. Jami'in diflomasiyyar ya ce akalla 'yan Sudan 2,500 ne suka yi zanga-zanga a harabar ofishin jakandanci Jamus da ke Khartoum, kuma akwai yiwuwar a samu karin wasu nan gaba. Sai dai ya ce kokari ne suke yi na ganin Sudan din ta sake komawa bisa mulkin dimukuradiyya sakamakon rudanin da ta fada ciki bayan kifar da gwamnatin kama-karya da tsohon Shugaba Omar al-Bashir a 2019.
Galibin wadanda ke kiraye-kirayen Kasashen Yamma su kwashe kayansu, su fice daga aksar ko kuma su daina sa baki cikin al'amuran kasar dai mabiya tsohon shugaban kasar Omar Hasan al-Bashir ne, wadanda jam'iyyarsu ta NCP ke da alaka da akidu na Islama, kuma suna yin hakan ne domin samun nasu kason a siyasar Sudan.
A makon jiya ne aka ruwaito cewa gamayyar kungiyoyin da ke fafutukar samar da sauyi a Sudan ta 'Forces of Freedom and Change, FFC' ta sanar da cewa akwai wata yarjejeniyar sake maido da kasar bisa mulkin dimukuradiyya.
Amma kuma akwai masu ganin ko da an maida kasar bisa mulkin na farar hula, da wuya ne a iya kawo karshen rigingimun siyasa a kasar a nan kusa, kamar yadda Kholood Khair, wata kwararriya kan siyasar Sudan ta nunar.
To sai dai ga jakadan Jamus a Khartoum ba lallai ba ne fassarar lamarin siyasar Sudan din ya kasance haka ba domin yana da yakinin cewa sannu a hankali daga mataki zuwa mataki, al'amura za su inganta har a kai ga samun daidaito a karshe a Sudan.