1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawa ta yi armashi tsakanin Koriya ta Kudu da ta Arewa

Ramatu Garba Baba
January 9, 2018

Kwalliya ta biya kudin sabulu a ganawar Jami'an Koriya ta Kudu da Koriya ta Arewa kan hadin kan da ake fata zai kai ga sulhunta rashin jituwar da ke tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/2qa7m
Südkorea Gespräche zwischen Nord- und Südkorea in Panmunjom
Tawagar jami'an Koriya ta Arewa da Koriya ta KuduHoto: IANS

Ganawa wadda ke zama ta farko tsakanin bangarorin biyu tun shekarar 2015, ministoci daga bangarori biyu ne dai suka jagoranci wakilai zuwa wajen wannan tattaunawa da ke cike da dumbin tarihi, Koriya ta Kudu dai ta yi amfani da wannan dama don kawo karshen zaman zullumi a mashigin ruwan Koriya, sakamakon matakin Shugaba Kim Jong-Un na Koriya ta Arewa kan bunkasa makaman nukiliya,

Lu Kang wanda shine mai magana da yawun ma'aikatar harkokin cikin gidan China ya ce sun dade suna jiran wannan rana inda a tattaunawa da manema labarai ya baiyana fatan ganin dorewar zama makamancin haka

Südkorea Nordkorea Gespräche in Panmunjom
Tagwar Jami'an kasar Koriya ta ArewaHoto: Reuters/Korea Pool

Mun sha fadin cewa a koyaushe muna marhabun tare da bayar da goyon baya kan duk wata tattaunawar zaman lafiya a tsakanin koriya ta arewa da koriya ta kudu muna kuma fatan wannan karon tattaunawar za ta kai ga samun hadin kai da ake bukata a kokarin cimma matsaya don kawo karshen duk wani sabanin da ke a tsakaninsu muna kuma fatan sauran kasashen duniya suma za su  yaba da wannan matakin

Ana dai kallon wannan shiri na tattaunawa tsakanin kasashen biyu a matsayin abu mai muhimmanci a kokarin samar da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu. Matakin sulhu dai abu ne da ake kallon baya ga inganta alaka tsakanin kasashen biyu wanda kuma  zai taimaka wajen kaucewa barazanar yaki da ake tunani.

A wani mataki na tabbatar wa duniya cewa da gaske su ke a ganawar an amince da bude kafar sadawar ta wayar tarho a tsakanin bangarorin biyu kamar yadda Chun Haesung ministan da ya wakilici Koriya ta Kudu ke cewa

A yayin tattaunawar Koriya ta Arewa ta shedawa takwararta  cewa ta bude hanyar sadawar tarho da ma'aikatar tsaro da ke kan iyakokinsu, tabbasa  mun kuma duba mun tabbatar da cewa an yi hakan, yanzu haka kofar sadawar tsakaninsu a bude ta ke.

Südkorea Gespräche zwischen Nord- und Südkorea in Panmunjom
Jami'an Koriya ta Arewa da Koriya ta KuduHoto: picture-alliance/AP Photo/Yonhap/Korea Pool

Tuni dai aka fara mayar da martani kan wannan ganawa, gwamnatin Japan na daya daga cikin kasashen duniya da ta soma tofa albarakacin bakinta duk da cewa ta kara yin jan kunne kan barazanar da duniya ke fuskanta a shirin bunkasa makamin nukiliya sai dai babban jami'in majalisar gudanarwa na kasar Yoshihide Suga ya ce ganawar abin yabawa ne

Muna maraba da sauyin hali na Koriya ta Arewa da amincewa da shiga gasar Olympics a birnin Pyeongchang. Amma maganar bunkasa makaman nulikiyar kasar har yanzu yana zama barazana ga kasashen wannan yanki da duniya baki daya, shi ya sa Majalisar Dinkin Duniya sanya mata takunkumi mai tsauri.

Tun a jawabin sabuwar shekara shugaban kasar Koriya ta Arewa, ya nuna yunkurin yin amfani da kakar wasannin Olympics mai zuwa da za a gudanar a Koriya ta Kudu don daidaita dangantaka tsakanin kasashen biyu bayan shekara guda da ya kwashe yana barazana da makaman kare dangi.