1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jaridun Jamus: Sulhu kan rikicin Sudan a Geneva

Zainab Mohammed Abubakar
August 16, 2024

Gwamnatin Sudan ta kaurace wa tattaunawar sulhu da Amurka ta kira, wadda aka fara a Geneva. A daya gefen kuma 'yan adawa na halarta

https://p.dw.com/p/4jZKU
Symbolbild Pressespiegel
Hoto: Jan Woitas/dpa/picture alliance

Jaridar die Tageszeitung ta wallafa sharhinta a kan kokarin da ake yi na warware rikicin Sudan. Jaridar ta ce a ranar Laraba ce a birnin Geneva a karkashin Amurka da Saudiyya a matsayin masu shiga tsakani da Switzerland a matsayin mai masaukin baki, Tom Perriello da ke zama jakadan Amurka a Sudan, ya tunatar da masu halartar taron cewa, akwai bukatar kawo karshen wahalar da yakin Sudan ya janyo, dole ne a mutunta dokar jin kai ta kasa da kasa domin barin isar da kayan jin kai ga mabukata, inda cikin kalmomi kalilan a shafinsa na X ya wallafa: "Lokaci ya yi da bindigogi za su yi shiru!"

Abdul Fattah Al-Burhan da Mohamed Hamdan Dagalo
Abdul Fattah Al-Burhan da Mohamed Hamdan DagaloHoto: Bandar Algaloud/Mahmoud Hjaj/AA/picture alliance

Sai dai bangarorin da ke fada da juna ba su halarci bude wannan taron ba. Gwamnatin Sudan ta yi watsi  da goron gayyatar da gwamnatin Amurka ta mika mata makonni uku da suka gabata, saboda tana son samun nasara a yakin da take yi da kungiyar mayakan sa-kai ta RSF, wanda aka fara tun watan Afrilun 2023.

A daidai lokacin da jami'an diflomasiyya ke hallara a birnin Geneva, shugaban kasar Sudan kuma hafsan sojojin Abdel Fattah al-Burhan ya sake nanata matsayinsa na kin amincewa da tattaunawar zaman lafiya muddin 'yan tawayen na ci gaba da cin karensu babu babbaka a cikin Sudan.

"Tunisiya na fuskantar barazanar sake komawa cikin zamanin Ben Ali" a cewar jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda ta wallafa labari kan halin da Tunisiya ke ciki a siyasance bayan da shugaba Kais Saied ya sa aka cire sunayen abokan hamayyarsa a jerin 'yan takara.

Shugaban Tunisiya Kais Saied
Shugaban Tunisiya Kais Saied Hoto: Chokri Mahjoub/ZUMA Wire/IMAGO

Jaridar ta ce tun kafin hukumar zaben kasar Tunisiya ta sanar da jerin sunayen 'yan takarar shugabancin kasar da za a gudanar a watan Oktoba, 'yan adawa da kungiyoyin farar hula sun yi ta furucin sukar yadda lamura suke tafiya. Zargin da suke yi shi ne cewar, ba a mutunta ka'idojin demokradiyya ba. An gindaya wasu sharudda da suka zama karan tsaye ga 'yan takarar kuma shugaba mai mulki Kais Saied yana amfani da damar ofishinsa wajen tallata takararsa. Kasancewar, baya ga Saied, wasu 'yan siyasa biyu ne kawai aka ba su damar tsayawa takara, ya tabbatar da haka.

Tun da farko, fiye da mutane 100 ne suka mika takardunsu na neman takara ga hukumar zabe. Mutane 17 daga cikinsu ne suka mika takardunsu a kan lokaci. Sai dai kuma yawancinsu ba su cika ka'ida ba, inji Farouk Bouasker, shugaban hukumar zaben Tunisiya. Baya ga takardar shaidar izinin 'yan sanda, sau da yawa ba a samu sa hannun masu goyon baya 10,000 da ake bukata.

Bisa la'akari da yanayin siyasar da ake ciki, da wuya a iya cimma wadannan sharuddan tun da babu walwala, in ji Neila Zoghlami, shugabar Kungiyar Matan Dimukuradiyya ta Tunisiya. 

Jimami kan cutar kyandar Biri a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo
Jimami kan cutar kyandar Biri a Jamhuriyar Dimukuradiyyar KongoHoto: Arlette Bashizi /REUTERS

Za mu karkare shirin na wannan makon da jaridar Welt Online wadda ta yi sharhi a kan ayyana bukatar daukar matakin gaggawa a bangaren kasashen duniya da hukumar kula da lafiya ta MDD a dangane da cutar kyandar biri da ta fara haifar da fargaba ga masu ruwa da tsaki a bangaren kiwon lafiya.

Jaridar ta ce WHO ta damu da yaduwar sabon nau'in da ake kira Mpox, wadda ta ayyana dokar ta-baci ta lafiya, duk da cewar har yanzu takaitattun wurare ne cutar ta bulla, sai dai akwai fargabar yaduwarta. Dalili kenan aka mike tsaye wajen fadakar da hukumomi a duniya don shirya bullar cutar da aka fi sani da cutar kyandar biri.

Sabon nau'in kwayar cutar da aka gano a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango a karshen shekarar 2023, na yaduwa tsakanin mutane. Ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike kan wannan cuta. Mutane fiye da 14,000 ne aka tabbatar da cutar a jikinsu a Kwango a wannan shekarar, kuma tuni mutane 524 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar)