1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sumamen sojojin Kamarun kan Boko Haram

Salissou BoukariFebruary 16, 2016

Dakarun sojan kasar Kamarun sun fatattaki mayakan Boko Haram a wani sumame da suka kai a wata maboyarsu da ke garin Ngoshe cikin Najeriya.

https://p.dw.com/p/1HwDj
Hoto: Reinnier Kaze/AFP/Getty Images

Dakarun sojan kasar ta Kamaru sun hallaka mayaka 162, tare da kwato dimbin kayayyaki da makammai a cewar mai magana da yawun gwamnatin kasar ta Kamaru. Wannan samanen dai ya waka na ne tun daga ranar 11 zuwa 14 ga wannan wata na Fabirairu a garin Ngoshe da ke cikin Nageriya a nisan km a kalla 15 da birnin Ashigashiya da ke iyakar Kamarun da Najeriya a yankin Arewa mai nisa a cewa Ministan yada labarai Issa Tchiroma Bakary.

Sai dai wasu daga cikin sojojin kasar ta Kamaru guda biyu sun rasa rayukansu inda daya daga cikinsu sakamakon nakiya da motar da yake ciki ta taka.

A halin yanzu dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan labari. Ministan ya kara da cewa a wannan sumaman sojojin na Kamarun sun samu kubutar da mutane a kalla 100 da aka yi garkuwa da su, cikin har da 'yan kasar ta kamarun 15.