1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sweden za ta dauki matakin shiga NATO

Abdul-raheem Hassan
May 15, 2022

Ana sa ran jam'iyyar Social Democrat da ke mulki a Sweden za ta dauki matakin shiga kungiyar NATO, lamarin da ka iya kawo karshen rashin jituwar sojojin kasar.

https://p.dw.com/p/4BJs1
Schweden | Patrouille schwedische Soldaten auf Gotland
Hoto: Karl Melander/TT/picture alliance

Jam'iyyar Social Democrat ta Sweden ta dade tana adawa da shiga NATO, inda take waswasin kar ta fada tsaka mai wuya, amma jami'iyyar ta cimma matsayar sake duba manufofinta.

Wannan dai na zuwa ne bayan tuni kasar jam'iyyar Social Democrat a Finland ta sanar da goyon bayanta ga shiga NATO a ranar Alhamis da ta gabata. Matakin da tuni kasar Rasha ta yi fara nuna 'yar yatsa. A halin da ake ciki, Zelenskyy na Ukraine ya rattaba hannu kan wata doka ta haramtawa jam'iyyun da ke goyon bayan Rasha.