1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Sweden za ta sayi tankokin yaki kirar Jamus

Abdullahi Tanko Bala
January 9, 2025

A wani gagarumin mataki na habaka tsaronta, kasar Sweden sabuwar mamba a kungiyar tsaro ta NATO ta shirya sayen tankokin yaki na Jamus samfurin Leopard

https://p.dw.com/p/4ozmf
Tankokin yaki kirar Jamus samfurin Leopard 2 A8
Tankokin yaki kirar Jamus samfurin Leopard 2 A8Hoto: Artur Widak/NurPhoto/picture alliance

Sweden za ta sayi tankokin yaki na Jamus samfurin Leopard 2 A8 guda 44 yayin da ta ke kokarin sabunta rumbun makamanta.

Ministan tsaro Pal Jognson ya ce Stockholm na fatan kashe kimanin euro miliyan dubu biyu domin inganta tsaron kasar.

Hukumar tsaron Sweden ta sanya hannu a kan yarjejeniya da kamfanin hadakar kera makamai na Jamus da Faransa KNDS kuma ana fatan fara mika makaman daga 2028 zuwa 2031.

Daga cikin makaman za a yi amfani da tankoki goma don maye gurbin tankokin da Sweden ta bai wa Ukraine gudunmawa.

Baya ga sabbin makaman da kasar za ta sayo za kuma ta gyara wasu tankokin 66 samfurin Leopard 2 da ta ke da su.