Taƙaddama tsakanin Pakistan da NATO na ƙara yin tsami
November 29, 2011Pakistan ta sanar da ƙaurace wa taron da za'a gudanar a birnin Bonn da ke tarayyar Jamus dangane da Makomar Afghanistan a mako mai zuwa. Wani jami'in gwamnatin Pakistan ne ya shaidar da hakan bayan ganawar majalisar zartarwar ƙasar a birnin Islamanad. Hakan dai na a matsayin martanin Pakistan dangane da harin sojojin ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO akan iyakokin Pakistan da Afganistan, daya kashe sojojinta 24.
Kafin cimma wannan matsayi a ɓangaren mahukunta a birnin Islamabad dai, mahukunta a birnin Washington sun yi kira ga Pakistan data halarci taron nemo hanyar warware matsalar Afganistan da zai gudana ranar 5 ga watan Disamba. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka a birnin Washington ya bayyana muhimmancin samun kyakkyawar danganta a tsakanin Amurka da Pakistan.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita Zainab Mohammed Abubakar