Taƙaddamar Turai da Rasha kan Ukraine
December 12, 2013A rikicin dake gudana tsakanin Ƙungiyar Tarayyar Turai da ƙasar Rasha kan Ukraine, shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin ya miƙa tayin shiga ƙawance a fiskar kasuwanci da ƙasar da ta taɓa kasancewa a tsohuwar daular Sobiet.
Babu wanda zai tilastawa wani yin abin da ba ya so amma idan har ƙasar Ukraine tana buƙatar ƙawa wadda za su yi aiki tare musamman wajen samar da haɗaka a fuskar haraji, Rasha a shirye take, bayanan da Putin ya yi ke nan a jawabin da ya kan gabatarwa ƙasa kowace shekara.
Mahukuntan Moskow sun daɗe suna zawarcin Kiev domin ta zo su yi aiki tare. Ƙungiyar haɗin kan harajin da ta girka a yanzu haka wanda kuma take mikawa Ukraine goron gayyatar shiga, tana da mambobin da suka haɗa da Kazakstan da Belarus, kuma Armeniya da Kyrgystan na shirin shiga.
Ma'aikatar cikin gidan Ukraine dai ta ce a yanzu haka akwai dubban masu adawa da shugaba Victor Yanukovich wanɗnda ke zaune a dandalin Indipenda cikin sanyin ƙanƙara suna zaman dirshen
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita : Umaru Aliyu