Ta yaya ake karɓar 'yan gudun hijira a Jamus
A wannan shekara ta 2015 hukumar kula da ƙaura ta Jamus ta yi ƙiayasin 'yan gudun hijira dubu 300, amma a yanzu sun kai dubu 450 waɗanda ke neman mafaka a Jamus. Shin yaya ake rarrabasu? Ga dai yanayin tsarin a jumulce.
Da farko watanni uku a cikin sanssanonin 'yan gudun hijira
A cikin rahoton da aka bayyana na waɗanda ke buƙatar mafaka a jihar Rheinland Palatinate da ke a yammacin Jamus , kimanin mutane 850 za a iya samarwa da matsugunai. Lokacin da 'yan gudun hijira suka iso Jamus a kan karɓesu a cikin cibiyoyi na wucin gadi inda za su yi zama na wani ɗan lokaci bayan watanni uku za a kai su wani gari ko wata unguwa. Kula da karɓar nasu ya danganta da wuraren.
Cibiyoyin gaggawa a ofishin birnin
Saboda yawancin cibiyoyin karɓar 'yan gudun hijirar sun cika makil, don haka ake amfani da wasu ofisoshi. A Hamm da ke a Nordrhein-Westfalen, da ke a yankin arewa ma so gabashin Jamus zauren taruka na Alfred-Fischer an mayar da shi matsugunin 'yan gudun hijira wanda kuma zauren kan ɗauki mutum 500. An dai raba zauren muhawarar mai faɗin murabba'in mita dubu 2700 gida biyu aka saka gadaje 14.
Domin kasancewa a wuri mai kyau
Cincirindon 'yan gudun hijirar da sannu a hankali na janyo gazawar biranen na ƙarɓarsu. Misali birnin Aachen da ke a yammacin Jamus a tsakiyar watan Yuli ya kamata ya karɓi 'yan gudun hijira 300. Kuma hanya ɗaya ta samar da isashen wuri ga kowa ita ce ta sakasu a cikin wata makaranta ta INDA, inda aka tsara agajin kiwon lafiya da gadaje da wurin kwana domin karɓar 'yan gudun hijirar.
Cibiyoyin da ba su daɗewa na wucin gadi
A baya- baya nan a nan Jamus a kan gina cibiyoyin 'yan gudun hijirar, inda ake gina wani garin na musammun da tantina. Buƙatar masu neman mafakan ta ƙaru a Halberstadt, Sachsen-Anhalt, da ke a yankin kudu ma so yammacin Jamusamma za a iya yin amfani da wuraren da ake da su kafin zuwan ɗari a samu wasu wuraren da ke da akwai.
Kamar dai a cikin sauran ƙasashe masu tasowa
Cibiya mafi girma ta 'yan gudun hijira wacce aka yi da tantina ita ce a halin yanzu wadda ke a Dresden.da ke a arewacin Jamus Rayuwa sai da haƙuri; jama'a kan ja dogon layi kafin samun shiga bayan ɗaki sannan akwai jira wajen samun abinci. Akwai mutane kusan dubu goma daga ƙasashe 15 da ke zaune a wurin, kuma ana sa ran a cikin kwanaki na gaba adadin mutane zai ƙaru har zuwa dubu goma sha ɗaya.
Rayuwa a cikin ɗakuna na kwanoni da aka gina
Domin ƙara adadin masu neman mafakar da sannu a hankali a kan gina ɗakuna kwanoni a Jamus a wurare daba-daban .Tun a shekarun 2014 aka fara gina waɗannan gidaje a cibiyoyin 'yan gudun hijira a Trier da ke a yammacin Jamus.
Hare-hare a kan cibiyoyin 'yan gudun hijira
'Yan kwana-kwana na kashe wutar gobara a cikin gidan wani ɗan gudun hijirar a Remchingen, Baden-Würtemberg, dake a yankin kudu ma so yammacin Jamus ranar 18 ga watan Yuli. Yanayin jama'ar ƙasar na Jamus na nuna ƙyama sosai ga 'yan gudun hijirar, a yanzu a kan kai hare-hare a kan 'yan gudun hijirar musammun ma a yankin gabashi da kudancin Jamus
Ƙorafin 'yan siyasa a cikin lamarin
Jagoran jam'iyyar SPD Sigmar Gabriel ya yi magana a kwanan baya yana mai cewar akwai 'yan gudun hijira kusan 300 a Wolgast, Mecklenburg da ke a arewacin Jamuswaɗanda ke yin rayuwa tare da ya'yansu.'Yan siyasa dai na buƙatar ganin gwamnatin ta taimaki jihohin da ke ɗaukar nauyin 'yan gudun hijirar da kuɗaɗe. Gabriel ya kuma ce maganar karɓar 'yan gudun hijira magane ce ta jin kai.
Sabbin gidajen kwana na 'yan gudun hijira
Domin biyan buƙatun 'yan gudun hijirar an gina sabbin gidaje da dama a Nuremberg da Bavaria da ke a arewacin Jamus da dai sauransu. Sabon wurin da aka gina a Nuremberg zai iya ɗaukar mutane 60 kuma za a fara yin amfani da shi a shekarun 2016.
Cibiyoyin sun fi zama na wucin gadi
An kammala sabbin gidaje da dama na 'yan gudun hijirar, za a ci gaba da gina gidajen yawancinsu na wucin gadi. Wasu ma'aikatan na ƙungiyoyi agaji su 170 sun gina wasu gidajen na tantina kusan 20 da kuma gadaje 300.