Ta'adin 'yan ta'adda kan kayayyakin tarihi
A karon farko kotun duniya mai hukunta masu manyan laifuka, tana duba lalata kayan tarihi, musamman ma barna a birnin Timbuktu na Mali. Amma ba nan kadai 'yan ta'adda suka yi ta'adi na kayan da suke da tsohon tarihi ba.
Birnin Timbuktu na Mali
'Yan tawayen Ansar-Dine masu da'awar jihadi sun lalata birnin na arewacin Mali mai tsohon tarihi a harkokin addinin Islama a shekara 2012. Sun bayar da dalilan na yadda wasu malamai ke girmama waliyai. Sannan sun kuma lalata hasumiyar masallatai na laka da suke birnin.
Birnin Timbuktu na Mali
Mutumin da yake kula da kaburbura na tarihi a Timbuktu. A wannan hoto na shekara ta 2014 yana addu'a kusa da daya daga cikin kaburburan da aka lalata. Abin da ke nuna sauyin da aka samu.
Birnin Timbuktu na Mali
Da yawa daga ciki za a iya sake ginawa da taimakon Majalisar Dinkin Duniya. Sane Chirfi (a dama cikin hoto) tare da iyalansa a waje mai tsarki da ake kira Alpha Moya.
Birnin Palmyra na Siriya
'Yan ta'addan IS masu kaifin kishin addinin Islama sun lalata birnin a shekara ta 2015, cikin abubuwan da suka lalata akwai wajen bauta na Bel da ya shekara 2,000, da kaburbura gami da gine-gine masu tsohon tarihi da dama. Mai daukar hoto a kusa da wajen bauta na Bel a shekara ta 2014. Bayan sake kwato birnin masu kula da kayan tarihi sun ji dadi. Kayayyaki da dama ba su lalace yadda ake zato ba.
Mar Elian na Siriya
Gini mai tsohon tarihi na Mar Elian yana da muhimmanci ga Kiristoci masu ziyarar ibada. Yana tsakiyar Siriya a birnin Karjatain wanda ya samo asali daga karni na 5.
Mar Elian na Siriya
A shekara ta 2015 tsagerun IS sun rusa Mar Elian. Hotunan Internet sun nuna yadda masu matsanancin ra'ayin suke rusa gine-ginen da manyan motoci. An sake kwato birnin. Sun kona kayan tarihin da ke ciki. Za kuma a sake gina Mar Elian.
Al-Hadra a Iraki
Al-Hadra ke zama babban birnin kasashen Larabawa na farko. Saboda irin manyan gine-gine da ya kunsa ya tsira daga mamayar Romawa a shekarun 116 da 198 Miladiya.
Al-Hadra a Iraki
A farkon shekara ta 2015 kungiyar IS ta lalata wani bangare na Al-Hadra. Wannan hoto ya fito daga faifan bidiyo na tsagerun da kamfanin dillancin labaran AP ya tantance sahihancinsa. 'Yan IS sun kuma lalata kayan tarihi masu muhimmanci a gidan tarihin da ke birnin Mosul na arewacin Iraki. Masu jihadin sun wace ta garin Nimrud da motocin rusa gine-gine.
Bamian-Tal a Afghanistan
Lardin Bamiyan ya kunshi manyan mutum-mutumi guda biyu na mabiya addinin Buddha. Mabiya addinin Buddha sun sassaka su da dutse kimanin shekaru 1,500. Tun kafin zuwan Musulunci Afganistan. A wannan hoton da aka dauka a shekarar 1973 mutum-mutumin mai tsawon mita 53 ne, wanda ke zama mafi tsawo a duniya a lokacin.
Bamian-Tal a Afghanistan
Tsagerun Taliban masu kaifin kishin Islama sun lalata mutum-mutumin guda biyu a shekara ta 2001. Sun yi amfani da tankokin yaki da makamai masu linzami gami da nakiyoyi. Amma ya ya dauki Taliban makwanni. Tun shekara ta 2003 masu kula da kayan tarihi suka saka kwazazzabon Bamian cikin kayayyakin tahiri na hukumar kula da ilimi, kimiya, da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO).