Tafsirin gidan Sarkin Kano yana daya daga cikin tafsiran Kur'ani da suka fi samun mahalarta a duk watan Azumi.Ya kafu tun shekaru 70 da suka gabata a zamanin da Sarkin Kano Muhammad Sanusi na daya yana ciroma a Chiranci inda ya mayar da shi gidan Sarki bayan da ya zama sarkin Kano a 1953.