Tahirin cutar Zika
June 8, 2016Talla
Kamar yadda hukumar lafiya ta nunar cutar Zika ta taba bulla a wasu kasashen Afirka. Amma yanzu haka cutar tun lokacin da ta bulla a Brazil ake neman matakan ganin an shawo kanta.
Masani kiwon lafiya sun gano cutar a karion farko a shekarar 1947 cikin yankin gabashin Afirka. Cutar tana cikin wadanda sauro yake yadawa. Tun lokacin da cutar ta Zika ta bulla a Brazil a shekara ta 2015 an tabbatar ta kama mutane 49, yayin da ake duba wasu 59 da ake zaton cutar ta kama su.