1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taimakon gaggawa ga Pakistan

August 19, 2010

Mutanen da ke buƙatar taimako a Pakistan sun kai miliyan takwas.

https://p.dw.com/p/OrtP
Wata matar da yayanta, cikin ruwa a PakistanHoto: AP

Majalisar Ɗinkin Duniya(MƊD) ta ce yawan 'yan Pakistan da ke buƙatar taimako gaggawa ya haura miliyan takwas. Majalisar ta ce waɗanda masifar ambaliyar ta shafa sun kai miliyan 15. Waɗanda suka rasa gidajensu kuwa, sun cimma miliyan huɗu da ɗari shida. A makon da ya gabata ne dai MƊD ta ƙaddamar da asusun neman taimako na Euro miliyan 360. I zuwa yanzu dai kashi 60 cikin ɗari ne kawai na wannan adadin aka samu, kuma dukkan kuɗin da aka bayar ba za su wadatar ba. Gwamnatin ƙasar Jamus, ta bayar da Euro miliyan 25 don taimaka wa Pakistan. Wannan ƙari ne kan Euro miliyan 43 da gwamnatin ta bayar tun farko cikin taimakon da Ƙungiyar Tarayar Turai(EU) ta aika wa Pakistan.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Halima Balaraba Abbas