1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashiya tana taimakon masu dimuwa a Kamaru

October 9, 2019

A kasar Kamaru wata matashiya 'yar shekara 28 aiki ta dauki kudurin fafutukan taimakawa masu dimuwa na matsalar kwakwalwa da rikicin 'yan a ware ya shafa.

https://p.dw.com/p/3Qywh
Schweiz Kamerun Protest in Genf
Hoto: pictre-alliance/AP Photo/Keystone/M. Trezzini

Franca Soulem ta shiga gidajen 'yan gudun hijira da ke fama da matsalar dimuwa da ya shafi kwakwalwansu a garin Yaounde. Yanzu haka yar shekara 28 da ke ziyartar mata da aka azabtar da su a fafutukan 'yan a ware masu magana da Turancin ingilshi a yankin kasar Kamaru.

Daya daga cikin wanda rikicin ya shafa y'ar shekara 45 Velma Arrey ta ce Franca ta ba ta goyon baya da kuma kwarin gwiwa yadda take so domin sake sabuwar rayuwa nan gaba. Ita dai Franca ta karanta fannin jarida a kasar Kamaru. A shekara ta 2018 ta tafi kasar Najeriya domin ci gaba da karatunta, tun wancan lokacin ta dauki kuduran taimakawa wadanda rikici ya shafa tun a lokacin da ta karanta wani labari kan wata 'yar gudun hijira da rikicin 'yan aware ya shafa a kasar Kamaru kan yadda ta sayar da jaririryarta sobada ba za ta iya kula da ita ba.

Ita dai mai shekara 28 da ke ziyarar wadanda rikicin ya shafa tana musu waka tana ba su labari kan kara musu kwarin gwiwa kan abu da ya faru da su da kada su yi danasani kan abun da ya faru a baya. Ta ce a rashin masu daukan nauyinsu tana karban kuncen kaya ga masu burin taimako sannan tana karban taimako domin taimaka musu. Da haka dai ita Franca da ke aikin fafutuka aka yi mata lakabi da uwar al'umma.