Takaddama akan shirin nukiliyar Iran
April 28, 2006A dai halin da muke ciki yanzu haka akwai sabani tsakanin manyan kasashen dake da dawwamammen wakilci a kwamitin sulhun. A yayinda Amurka ke neman ganin an kakaba wa Iran takunkumi, kasashen Rasha da China na adawa da haka. Za a cimma tudun dafawa domin warware wannan rikici ne ta hanyar shawarwari na keke da keke tsakanin Iran da Amurka. A sakamakon matsin lamba daga Amurka kwamitin sulhu na MDD ya bai wa Iran wa’adin kwanaki 30 domin ta dakatar da matakinta na tace Uranium da inganta shi domin sarrafa makaman kare dangi. Amma sanin kowa ne cewar har abada Iran ba zata yarda ta ba da kai bori ya hau ga wannan matsin lamba ba. A maimakon haka kasar Iran fitowa tayi tana mai buga kirjin cewar ta samu nasarar tacewa da inganta ma’adanin na Uranium kuma zata ci gaba da tafiya akan wannan hanya da ta kama. Ga mashawartan fadar mulkin Amurka ta White House, wannan bayani ne dake tattare da takaici. Saboda ba daya daga cikinsu da yayi zaton cewar akwai wata kasa da zata nuna irin wannan taurin kai ga babbar daular ta duniya. Amma fa shi kansa wa’adin kwanaki 30 da aka tsayar wata alama ce ta gazawa. Shekaru uku cir aka yi a jere ana wa Iran barazana, sai kuma ga shi a karshe an kasa cimma daidaituwa akan wani matakin da za a iya dauka kanta. Kwanaki 30 din da aka kayyade mata bai tsinana kome ba. Kasashen Rasha da China zasu ci gaba da hana ruwa gudu a game da duk wani matakin da za a dauka kan kasar Iran, musamman ma idan ya shafi wani mataki na soja. Abu daya da zai fid da Amurka kunya dai shi ne ta nemi tuntubar juna kai tsaye da kasar Iran, kamar yadda tayi dangane da Koriya ta Arewa. Amma Amurkan ba ta sha’awar yin haka. Da farko fadar mulki ta white House ta bayyana shirinta na tattaunawa da Iran a game da zaman lafiyar kasar Iraki, amma a lokacin da Iran ta ce a shirye take ta tattauna akan wannan batun, sai gwamnati a birnin Washington ta sa kafa tayi fatali da lamarin. Duka-duka abin da Amurka ke fatan gani shi ne ta ga an kawar da gwamnatin dake ci yanzu haka a birnin Tehran. Ganin cewar da wuya hakan ya samu ne kasar ta Amurka ta fara barazanar daukar matakan karfin hatsi akan kasar Iran, abin da ya hada har da yiwuwar amfani da makaman nukiliya. Amma fa kwamitin sulhu na MDD ba zai amince da wannan shawara ba duk da rashin cimma biyan bukata bayan kawo karshen wa’adin na kwanaki 30. Bugu da kari kuma hatta masu goya wa Amurka baya a game da takunkumi kan Iran suna cikin hali na kaka-nika yi saboda sune zasu fi jin radadin matakan na takunkumi. Dangane da matakan soja kuwa ba zai tsinana kome ba illa ya kara tsawwala mawuyacin halin da ake ciki a shiryar ma gaba daya. Ta la’akari da haka lokaci yayi da kasashen Turai zasu daina zama ‘yan rakiya ga kasar Amurka. Wajibi ne su nemi wata ganawa ta keke da keke tsakanin kasashen na Amurka da Iran kamar yadda lamarin ya kasance dangane da Koriya ta Arewa tare da mayar da hankali wajen neman fahimta da kusantar juna domin ta haka ne kawai za a cimma tudun dafawa wajen shawo kan wannan takaddama da ta ki ci ta ki cinyewa.