Takaddama kan Bankin da babu ruwa cikinsa a Nigeria
July 5, 2011A Wani muhimmin mataki na kara wayar da kan jama'ar ƙasar game da tsarin Bankin da babu ruwa a cikinsa, da ake shirin kafawa a Nigeria, babban Bankin ƙasar ya shirya wani taron masu ruwa da tsaki a harkar domin dai kawar da takaddamar da ta taso a ƙasar tun bayan shelar fara amfani da wannan tsari,
Yayin taron dai masana sun yi fashin baki akan tasirin Bankin da ma ribar da zai iya kawowa ga tattalin arzikin Nigeria. Kamar yadda wakilin mu na Abuja Uwais Abubakar idris ya aiko mana.
To akan wannan batu na kafa bankin da babu riba acikinsa, daga nan Bonn abokin aikina Salisu Nasiru Zango ya tuntubi farfesa chika Umaru Aliu, na sashin tsimi da tanadi a jamiar Usman ɗan Fodio da ke Sokoto a Nigeria, wanda yayi bayani akan wannan batu, da fari dai farfesan ya fara ne da shimfida akan yadda tsarin Bankin musulunci yake, da ma bambamcinsa da salon tsarin banki ba tare da kuɗin ruwa ba.
Mawallafiya: Nasiru Salisu Zango
Edita : Zainab Mohammed Abubakar