1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin kotu kan takaddamar Iran da Amurka

March 30, 2023

Babbar kotun kasa da kasa ta yi watsi da bukatar da Iran ta shigar a gabanta ta neman cire wasu kudaden bankunan kasar da Amurka ta rike.

https://p.dw.com/p/4PWWu
Niederlande Internationaler Strafgerichtshof in Den Haag
Hoto: Peter Dejong/AP Photo/picture alliance

 

Babbar kotun mai ofishinta a birnin Hague na kasar Netherlands, ta yi watsi da bukatar ta Iran ta neman cire dala biliyan biyu daga cikin kudaden kasar da Amurka ta rike bayan makara mata takunkumi kan aikin ta'addanci.

Sai dai a daya gefe kuma kotun ta ce Amurka ta keta doka tare cin hakkin 'yan kasar Iran wajen kame masu kudade da ta yi.

Amurika dai na tuhumar Iran da hannu a jerin hare-hare da dama da aka kai a cikin kasar da kuma sansanonin sojinta da ke wasu kasashe, wannan ne ma ya sa a shekarar 2016 kotun Amurkar ta yanke hukuncin a yi amfani da kudaden bankunan na Iran wajen biyan diyya ga wadanda aika-aikar da kasar ta yi ko take da hannu a ciki ta shafa.

Tun dai shekarar 2016 fadar Tehran ke fafitkar karbar wadannan kuden domin jurewa takunkuman da kasashen Yamma suka kakaba mata kan shirinta na nukiliya.

A halin yanzu dai kotun da ke karkashin majalisar dinkin duniya ta ba wa Iran da Amurka wa'adi na watanni 24 na su daidaita kansu kan yadda za a biya diyya ga ma'aikatu da kuma mutanen da hare-haren ta'addanci da Iran ke da hannu a ciki ya ritsa da su.