1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama kan zaben gabashin Ukraine

Jane McintoshNovember 3, 2014

Tarayyar Turai da Amirka sun yi watsi da zaben da 'yan aware na gabashin Ukraine suka shirya tare da lasheshi.

https://p.dw.com/p/1Dfuw
Ostukraine Wahlen Telmanove 02.11.2014
Hoto: Alexander Khudoteply/AFP/Getty Images

Kasashen Turai da Amirka da kuma Ukraine sun yi watsi da zaben da 'yan awaren gabashin Ukraine suka shirya a wannan Lahadi da ta gabata, amma Rasha ta nemi a mutunta zaben al'ummar yankin kudu maso gabashin Ukraine.

Hasashe ya nuna cewa Alexander Zakharchenko shugaban 'yan awaren ya samu kashi 81 cikin 100 na kuri'un da aka kada, abin da ake gani zai kara tabarbara lamura tsakanin 'yan awaren da Shugaban Ukraine Petro Poroshenko.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe