Yuganda: Takaddama ta barke kan sakamakon zabe
February 20, 2016Hukumar zaben kasar ta Yuganda dai ta bayyana Museveni a matsayin wanda ya lashe zaben da sama da kaso 60 cikin 100 na kuri'un da aka kada. Kizza Besigye wanda aka bayyana a matsayin wanda ya zo na biyu a zaben shugaban kasar da sama da kaso 35 cikin 100 na kuri'un da aka kada, ya bayyana sakamakon zaben da cewa abin kunya ne
A wata sanarwa da ya fitar Besigye ya bayyana cewa sun shaida zaben da ya fi ko wanne rashin inganci a Yuganda, kana ya bukaci da aka gudanar da sahihin bincike kan sakamakon.
Hukumar zaben kasar Yuganda ta bayyana shugaban kasar mai ci a yanzu Yoweri Kaguta Museveni a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Alhamis din da ta gabata. Lateefa Mustapha Ja'afar ta hada mana rahoto kan wannan batu.
Shugaba Yoweri Museveni dai ya kwashe tsahon shekaru ya na mulkin kasar ta Yuganda, kana a yanzu ma ya samu nasarar yin tazarce da kimanin kaso 60 cikin 100 na kuri'un da aka kada, yayin da dan takarar jam'iyyar adawa ta Forum for Democratic Change, Kizza Besigye da rahotanni suka bayyana cewa ko da a ranar zabe sai da jami'an tsaron kasar suka cafke shi ke bi masa da kimanin kaso 35 cikin 100 na kuri'un da aka kada. Da yake bayyana sakamakon zaben, shugaban hukumar zaben kasar ta Yuganda Badru Kiggundu, ya ce Museveni ya samu nasarar yin tazarce da gagarumin rinjaye.
Akwai dai korafe-korafe masu yawa musamman na zargin tursasawa da ma yin magudi daga bangaren 'yan adawar kasar ta Yuganda. Koda masu sanya idanu a zaben na kungiyar Tarayyar Turai wato EU ma sun zargi hukumar zaben kasar da aikata kura-kurai.
Wakilan kungiyar ta EU karkashin jagorancin Eduard Kukan sun zargi hukumar zaben ta Yuganda da cewa ba ta yin aikinta kamar yadda ya kamata a matsayinta na hukuma mai zaman kanta ba, yana mai cewa:
Shugaban tawagar sanya idanu a zaben na kungiyar EU Eduard Kukan wanda ya bayyana matsayar tawagar tasa daga Kampala babban birnin kasar ta Yuganada, ya kuma yaba da kokarin al'ummar kasar bisa nuna juriya da suka yi wajen fitowa domin kada kuri'unsu a zaben na shugaban kaa da na 'yan Majalisu. sai dai Kukan ya koka kan yadda 'yan sanda suka yi amfani da karfi wajen kamewa tare da tsare madugun 'yan adawar kasar Kizza Besigye, wanda ya samu mataki na biyu a zaben shugaban kasa. Su ma a nasu bangaren masu sanya idanu na kungiyar kasashe rainon Ingila wato Commonwealth sun yi irin wannan korafi. A nata bangaren kuwa kasar Amirka bukata hukumomin Yugandan ta yi kan su mutunta 'yancin dan Adam musamman ma 'ya'yan jam'iyyun adawar kasar da ke yin korafin ana tursasa musu.