1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China ta musunta yi wa Burtaniya leken asiri

Abdourahamane Hassane
September 11, 2023

Mutumin da ake zargi da yin leken asiri a majalisar dokokin Burtaniya bisa umarnin kasar China, ya bayyana cewa ba shi da wani laifi.

https://p.dw.com/p/4WDQO
Hoto: Zoonar/picture alliance

Lamarin dai ya sake tayar da jijiyoyin wuya tsakanin Burtaniya da Chinar wacce ta yi  watsi da zarge-zargen da ta ce marasa tushe ne. Wadannan zarge-zargen na leken asiri na zuwa ne a daidai lokacin da Birtaniyar ta nuna sha'awar tattaunawa da China a baya-bayan nan, bayan shafe shekaru da dama kasashen biyu ba su dasawa.Rundunar ‘yan sandan Burtaniya ta sanar a ranar Asabar din da ta gabata cewa ta kama wani mutum mai shekaru ashirin a cikin watan Maris a gidansa da ke Edinburgh bisa laifin leken asiri, ba tare da bayyana sunansa ba, ko kuma bayar da cikakken bayani kan ayyukansa .