1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama tsakanin Rasha da Amirka kan rikicin Siriya

Mahmud Yaya Azare RGB
June 21, 2017

Duk da gargadin da Rasha ta yi wa Amirka na yiwuwar raba gari da ita a yakin murkushe IS, Amirkar ta sake harbo wani jirgin yakin Siriya.

https://p.dw.com/p/2f7Qo
US Luftwaffe - Super Hornet Start
Hoto: Reuters/U.S. Navy/Mass Communication Specialist 2nd Class Ryan U. Kledzik/Handout

Jirgi na biyun da Amirkar ta kakkabo a cikin mako guda a kasar ta Siriya jirgi ne mai sarrafa kansa kirar kasar Iran. Jami'an Amirka sun ce a yanzu suna dab da tabbatar da ko rundunar juyin juya hali ta kasar Iran ce ta sarrafashi, bayan da ta ayyana fara kai hare-haren ramuwar gayya kan kungiyar IS a cikin Siriya, wacce ta kai wasu hare-haren ta'addanci cikin kasar ta Iran makwanni biyun da suka gabata.

Rundunar Sojin Amirkar dai ta futo karara ta bayyana cewa duk wani harin da za a kai wa Kurdawan da take ba wa kariya tamkar hari ne kanta.

Syrien Demokratische Kräfte Syriens bei Raqqa
Mayakan kungiyar Syrian Democratic Forces da ke samun goyon bayan AmirkaHoto: picture-alliance/AP Photo/Syrian Democratic Forces

A nata gefen rundunar sojin Rasha wacce ta siffanta kakkabo jiragen na Siriya da neman tsokana, ita ma ta yi barazanar kakkabo duk wani jirgin kawancen da ya keta kudancin kogin Furat, bayan da ta ayyana dakatar da tuntubar junan da take da Amirkar a yakin da suke da kungiyar IS.

Kawancen yaki da IS na fuskantar barazana

Tuni dai kasar Ostareliya ta sanar da ficewa daga kawancen da Amirka ke jagoranta na yaki da IS biyo bayan gargadin na Rasha.

Gwamnatin Siriya wadda a sannu sannu dakarunta ke kwato wuraren da suka kubuce musu a baya, ta ce kakkabo jiragen nata biyu babbar shaida ce kan yadda Amirka ke bada kariya ga 'yan ta'adda.

Masharhanta na tabbatar da cewa, duk wani taho mu gaman da za a samu a Siriya tsakanin Amirka da Rasha ba zai haifarwa kasar ta Siriya da mai ido ba.