Takaddamar Kosovo da Serbiya
September 16, 2011Babban Sakataren kungiyar tsaro ta NATO Anders Fogh Rasmussen ya ce kawancen ba za shi bar takadammar da ke tsakanin Serbiya da Kosovo ta tabarbare ba.
A wannan juma'ar ce ake sa ran hukumomin Kosovo zasu karbi ikon kulawa da iyakokinsu daga dakarun NATO duk da irin barazanar da suke fuskanta daga Serbiyawan da ke zama a yankin.
A watan Yulin da ya gabata, wani dan sandan Kosovo, daga kabilar Albaniyawa ya hallaka, lokacin wata taho mu gama da ta afku tsakanin jami'an 'yan sandan da Serbiyawan yankin, wadanda suka yi adawa da wani shiri na mika ikon iyakokin makamancin wannan-Kuma Serbiya ta yi gargadin cewa hakan ka iya sake afkuwa. Tun a watan Yulin ne dai dakarun NATOn ke kula da iyakokin amma ana sa ran zasu mika iko a wannan juma'ar.
Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita: Yahouza Sadissou Madobi