Rikicin Siriya ya yi sanadiyyar rayuka dubu 250
July 29, 2015Staffan de Mistura ya fada wa Kwamitin Sulhu cewar, fatan Majalisar Dinkin Duniya shi ne, lokacin da Siriyawan za su bayyana a wurin taron, suna da kyakkyawan guzuri dangane da makomar kasarsu a siyasance, musamman yadda za a warware rikicin.
A cewarsa muhimmin abun da aka cimma a taron sulhu tsakanin manyan kasashe a watan Yunin 2012, shi ne kafa gwamnatin rikon kwarya mai cikakken iko. Hakan shi ne tubali, kafin a gudanar da zabe, wanda zai bukaci shugaba Bashar al Assad ya mika mulki a wani lokacin da ba a zartar ba.
Babban sakataren MDD Ban Ki moon, ya fada wa Kwamitin Sulhun cewar, rikicin na Siriya da ya dauki sama da shekaru yana gudana, wanda ya lashe rayukan mutane a kalla dubu 250, alamu ne na gazawar al'ummomin kasa da kasa saboda rarrabuwar kawuna da ke tsakaninsu a kan rikicin.