1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kafa Majalisar Dinkin Duniya a 1945

Salissou Boukari
November 7, 2016

A ranar daya ga watan Janairu na 1942 ne aka soma ambato batun kafa Majalisar Dinkin Duniya, kuma shugaban kasar Amirka na wancan lokaci Franklin D. Roosevel, shi ne ya bada wannan shawara.

https://p.dw.com/p/2SH0w
U.N. Secretary General Ban Ki-moon stands during meeting at United Nations headquarters in New York
Hoto: Reuters/M. Segar

Kalmar ta fito ne a lokacin yakin duniya na biyu, kuma an yi amfani da ita a karo na farko wajen sanarwar da kasashen suka fitar a ranar daya ga watan Janairu na 1942 sanarwar da a cikinta wakillan kasashe 26 suka dauki alkawarin hadin kai domin cigaba da yakar manyan kasashe masu danniya. 

A ranar 24 ga watan Octoba na 1945 Sir Laurence Olivier dan wasan fina-finai dan kasar Britaniya ya karanta dokokin da wadannan kasashen suka yi, wanda shi ne mafarin kafuwar kungiyar Majalisar Dinkin Duniya inda a lokacin bazara na 1945, wakillai na kasashe 50 suka hadu a wani babban zaman taro da aka yi a birnin San Francisco na kasar Amirka, domin a samu tsara dokokin kungiyar ta Majalisar Dinkin Duniya, kuma shawarwarin da wakillan kasashen Chaina, Amirka, Britaniya, da Tarayyar Soviet suka gabatar a tsakanin watan Augusta zuwa Octoba na 1944 a birnin Oaks na kasar Amirka, sun taimaka sosai ga wannan aiki na samar da dokokin, inda a watan Yuni na 1945, wakillan wadan nan kasashe 50 suka rattaba hannu kan wannan kundin dokoki na kungiyar.

A ranar 24 ga watan Octoba na wannan shekara ta 1945 ne aka kaddamar da kungiyar Majalisar Dinkin Duniya, bayan da kasashe irin su Chaina, Amirka, Britaniya, Tarayyar Soviet a wancan lokaci, da kuma mafi yawan sauran kasashen da suka rattaba hannu na amincewa da kungiyar. Kuma tun wannan lokaci ake gudanar da bukukuwan zagayowar ranar Majalisar Dinkin Duniya a duk ranar 24 ga watan Octoba na ko wace shekara.

 

Sunayan wadanda suka jagorancin Majalisar Dinkin Duniya

-Gladwyn Jebb:  Dan kasar Britaniya wanda ya yi rikon kwarya kafin lokacin zabe daga ran 24 octobre 1945 zuwa daya ga watan février 1946.

-Trygve Lie: Dan kasar Norvege wanda aka zaba a matsayin Sakatare Janar na farko daga ranar 2 ga watan Febrairu na 1946,  zuwa 10 ga watan Nuwamba na 1952 wanda kuma ya yi murabus a yayin da yake cikin wa'adin shugabanci na biyu.

-Dag Hammarskjöld: Dan kasar Sweden wanda ya jagoranci kungiyar ta Majaliyar Dinkin Duniya daga ranar 10 ga watan Afirilu na 1953 zuwa 18 ga watan Satumba na 1961 kuma ya rasu a lokacin yana kan wa'adin mulkinsa na biyu.

-U Thant: Dan kasar Birmaniya ya rike wannan mukami na Sakatare Janar daga 30 ga watan Nuwamba na 1961 zuwa 31 ga watan Disamba na 1971 kuma ya cika wa'adi biyu na shugabanci.

-Kurt Waldheim: Dan kasar Ostriya ya rike mukamin daga daya ga watan Janairu na 1972 zuwa 31 ga watan Disamba na 1981 shi ma ya yi wa'adi biyu na mulki.

-Javier Pérez de Cuéllar: Dan kasar Peru ya jagoranci kungiyar daga daya ga watan Janairu na 1982, zuwa 31 ga watan Disamba na 1991 shima ya cika wa'adi biyu.

-Boutros Boutros-Ghali: Dan kasar Masar ya yi jagoranci daga daya ga watan Janairu na 1992 zuwa 31 ga watan Disamba 1996 yayi wa'adi daya na shugabanci.

-Kofi Annan: Dan kasar Ghana, ya yi shugabanci daga daya ga watan Janairu na 1997 zuwa 31 ga watan Disamba 2006, ya yi wa'adi biyu na shugabanci.

-Ban Ki-moon: Dan kasar Koriya ta Kudu ya karbi shugabancin ne daga du ranar daya ga watan janairu na 2007 inda zai kawo karshen wa'adin mulkinsa na biyu a ranar 31 ga watan Disamba na 2016.

Sai kuma sabon Sakataran Majalisar ta Dinkin Duniya ma jiran gado António Guterres, wanda zai kama aiki daga ranar daya ga watan Janairu.