Takaitaccen tarihin kungiyar tafkin Chadi
August 10, 2016Ita dai kungiyar da ke kula da tafkin Chadi ta CBLT, an kafa ta ne a ranar 22 ga watan Mayu na 1964, kuma shugabanni na wancan lokaci da suka kafa wannan kungiya, sun hada da Ahmadou Ahidjo na Kamarun, da N’Garta Tombalbaye na kasar Chadi, Hamani Diori na Nijar da kuma Tafawa Balewa na Najeriya. Sai dai daga bisani yawan membobin kungiyar ya karu ya zuwa shida bayan da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta shiga cikin kungiyar a shekarar 1996 da kuma kasar Libiya a shekara ta 2008. Sannan kasashe kamar su Sudan, Masar, da Jamhuriyar Kwango Brazzaville da kuma makwabciyarta Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango da suke a matsayin membobi amma masu sa'ido. kuma cibiyar kungiyar na a Ndjamena babban birnin kasar Chadi.
Burin da kungiyar ta sama gaba
Babban burinta shi ne na kula da ciban wannan tafki ta hanyar samar da daidaito tsakanin kasashe, tare da kare shi daga duk wasu kalubale da za su haddasa masa koma baya, sannan da abin da ya shafi tsaro da zaman lafiya a kan iyakokin kasashen yankin na Tafkin Chadi. Kuma wannan kungiya ta CBLT na a matsayin memba ga hadin gwiwar kungiyoyin kasashen Afirka masu kula da tsarin tabakuna da aka wa suna ROAB, da kuma kungiyar duniya mai kula da tsarin tabakuna mai suna RIOB. Kungiyar ta tafkin Chadi na samun kudadan shigarta ne na farko daga gudunmowar da kowace kasa memba ke bayar wa, amma kuma a halin yanzu kungiyar na cikin nazarin samun tsarinta na kanta na samun kudade.
Lokacin da aka kafa wannan kungiya, tafkin na Chadi yana da fadin murabba'in km 25.000, amma ya zuwa shekara ta 2010 fadinsa ya koma kimanin murabba'in km 2000 daga dubu 25 an komo 2000. Yankunan da wannan tafki na Chadi ya kumsa sun kai fadin murabba'in km 967.000. kuma sun hada da jihohi uku na kasar Kamarun, jihoji biyu na Nijar, jihohi shida na Najeriya, da jihohi uku na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sannan da illahirin fadin kasar Chadi. Tafkin ya na da kananan rassa da ke haduwa da shi kamar wadanda ake kira Logone, Chari, El-Beid, Komadougou-Yobe, Yedsaram, Ngadda, Serbewel, da kuma Taf-taf.
Yawan al'ummar da ke cin moriyar wannan tafki?
An kiyasta yawan al'ummar da ke kewayan na yanki tafkin Chadi ga mutane a kalla miliyan 30 da suka hada 'yan kasar Kamarun, Nijar, Nijeriya, Chadi, da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Kuma al'ummomin wannan yanki sun kasance ne 'yan kabilar Kanouri, da Mobber, da Boudouma, da Haussawa, a kwai Kanembu, Kotoko, Shuwa Arab, Hadda, Kouri, Fulani, da Mangawa wadanda dukkanninsu suke aiyyuka na kamun kifi, ko noma da sauran kasuwanci.