1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaitaccen tarihin rayuwar Hama Amadou

Salissou Boukari
October 24, 2024

Allah ya yi wa tsohon firaministan Nijar kuma tsohon shugaban Majalisar dokoki Hama Amadou rasuwa yana da shekaru 74 da haihuwa.

https://p.dw.com/p/4mCAl
Hama Amadou
Hoto: Imago/W. Prange

Hama Amadou tsohon firaminista kuma tsohon shugaban majalisar dokoki ya kasance daya daga cikin manyan yan siyasar Jamhuriyar Nijar. A baya marigayi Hama Amadou ya rike mukamai dabam-daban kama daga na shugaban gunduma da ake kira sous-préfet a wancan lokaci, sannan ya rike mukamin Darectan fadar shugaban kasa marigayi Seyni Kounche, ya rike mukamin Darecta Janar na gidan radio da talbijin na kasa ORTN, ya zama Minista kafin daga bisani a nada shi firaministra a shekara ta 1995 lokacin mulkin marigayi Tanja Mamadou na tsawon shekaru bakwai.

Karin Bayani: Nijar: Ina makomar Jam'iyyar PNDS Tarayya?

Hama Amadou a lokacin kada kuri'a
Hoto: Getty Images/AFP/Seyllou

A fagen siyasa marigayi Hama Amadou ya taka rawar gani tun daga muhawara ta kasa. Ya rike matsyin dan majalisar dokoki na kasa sau da dama kafin ya zama shugaban majalisar dokoki a shekara ta 2013 bayan da ya dafa wa Mahamadou Issoufou ya samu mulki a shekarar 2011 kafin daga bisani su raba gari inda a shekarar 2016 daga gidan kaso Hama Amadou ya yi takarar neman shugabancin kasa tare da shugaban kasa na wancan lokaci Issoufou Mahamadou, inda aka tislata masa barin kasar ya yi gudun hijira zuwa kasar Faransa, sai bayan juyin mulkin da aka yi ne na ranar 26 ga watan Yulin 2023 marigayi Hama Amadou ya samu sukunin shiga komawa kasarsa ta Nijar ba tare da wata matsala ba.

Karin Bayani: Madugun adawa Hama Amadou ya koma gida

Hama Amadou a majalisar dokoki
Hoto: DW/Mahamman Kanta

Makusantan Hama Amadou sun ce har Allah ya karbi rayuwarsa kullum da yamma sai ya je motsa jiki, kuma Direbansa Habibou Midou ya ce wannan ne ma abu na karshe da yake tunawa game da marigayin:

Mamane Saminou Abdou ya ce tare suke tattakin motsa jiki da marigayi Hama Amadou a cibiyar horas da yan kwallo ta FeniFoot:

Abdou Raffa shi ne jami'in hulda da jama'a na marigayin ya ce ya samu labarin rasuwar maigidansa kuma abokinsa Hama Amadou lamarin da ya tayar masa da hankali sosai:

Karin Bayani: Nijar: An fitar da Hama Amadou zuwa Faransa

Hama Amadou da Mahamadou Issoufou
Hoto: BOUREIMA HAMA/AFP/Getty Images

Daga cikin yan siyasa kuma masu sharhi kan al'amuran yau Soumaila Amadou ya ce rasuwar Hama Amadou ba karamin rashi ne ga jamhuriyar Nijar ba:

A ranarJumma'a nei za a yi jana'izar marigayi Hama Amadou inda bayan an dauki gawarsa za a kaita fadar shugaban kasa domin karramawa, kafin daga bisani a fice da ita zuwa mahaifarsa Youri da ke da nisan kilomita 40 daga jihar Tillabery.