1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takarar mata a zaben 'yan majalisa a Nijar

Issoufou Mamane/GATJanuary 6, 2016

A karon farko tun bayan soma zabuka kan tafarkin Demokradiyya a Nijar mata da dama sun sha alwashin tsayawa takarar neman mukamin 'yan majalisa da na kansiloli a zabuka gama gari na 2016

https://p.dw.com/p/1HZOM
Niger Wahlen Politik Stimmen Auszählung
Hoto: DW/M. Kanta

A jamhuriyar Nijer, a dai dai lokacin da kasar ta shirye-shiryen gudanar da zabukan gama gari, a karon farko an samu karuwar mata 'yan takara a zaben majalisar dokoki da na kansiloli abin da ke zaman wata babbar nasarar da matan suke alfahari da ita ga gwagwarmayar neman 'yincinsu a kasar.

Sama da shekaru 30 da suka shude, ganin macce na neman matsayi a siyasance na zaman mafarki dubi da matsayin da aka ba su na kananan madafun iko a kasar.

Matan Nijar za su fafata da maza a zaben 'yan majalisa na 2016

To amman tun bayan taron kasa na ''Conference Nationale'', sannu a hankali hakar tasu ta fara cimma ruwa inji Hajiya Umma Ali daya daga cikin jagororin kungiyar mata:

Flash-Galerie Wähler in einem Wahllokal in Niger
Hoto: AP

"Lalle mata akwai cigaba garemu ta fiskar siyasa dai. Ka san a da tafe ne mu ke kara zube, amma daga baya sai aka fito da doka da ta tanadi ba mu wani kaso. A baya macce na jin tsoro ta tsaya takara a gaban namiji. To sai aka wayi gari a siyasance wani guri muna ma finsu iyawa.Kuma wasu matsalolin da mata ba sa iya fada wa maza a yanzu ta samu damar iya bayyana su ga 'yan uwarta macce kuma asirinsu rufe ta ba ta mafita"

Da dama dai daga cikinsu na amfani da kalmar ''kwato 'yincin takwarorinsu matan da ma yara'' da zaran sun kai ga gacci inrinsu Mme Suleiman Hajiya Rabi Hassan Maifada:

"Nan kasarmu ta Nijar mu mata mun fi yawa, kuma da dama daga cikinmu muna gwagwarmaya tare da maza,amma mu ke taimakonsu muna jefa masu kuri'a.To wannan ta sanya na yanke shawarar nima in tsaya takara dan in amso 'yancin mata 'yan uwana. Kuma in Allah ya yarda muna takara da suna mata da kuma matasa domin shirya masu makoma a matsayinsu na manyan gobe"

Wähler vor Wahllokal in Tahoua Niger
Hoto: DW

Matan Nijar na kawo goyon bayansu ga mata 'yan takara

Wannan sabon matsayin da matan ke samu a siyasance ke basu kwarin gwiwar alfahari inji Mme Ali hajiya Abarta:

" Yau mun yi wa Allah godiya da ya bamu 'yar takara mace. Kuma kirana ga diya mata shi ne a ranar zabe mu zamo tsintsiya madaurinki daya dan mu zabi 'yan uwarmu mace"

Abin jira a gani a nan gaba shi ne rawar da matan kasar ta Nijar za su taka a wannan karo a kokarinsu na zama 'yan majalisa ko kuma kansaloli a kasar ta Nijar.