1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takarar Sabiya ta shiga EU ta ci karo da adawar Romaniya

February 29, 2012

Kasar Romaniya ta ki amincewa da bukatar Sabiya ta ajje takarar zama memba a rukunin kasashen Kungiyar taraya Turai

https://p.dw.com/p/14C0r
Serbia's President Boris Tadic (L) and European Commission President Jose Manuel Barroso (R) hold a joint news conference after a meeting in Brussels February 28, 2012. Romania threatened on Tuesday to derail European Union plans to grant Serbia membership candidate status in a row over minority rights in the former Yugoslav state, EU diplomats said. REUTERS/Eric Vidal (BELGIUM - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Kasar Romaniya ta kawo cikas a yunkurin Sabiya na ajje takara zama memba a rukunin kasashen kungiyar tarayya Turai.Ministan harakokin wajen Jamus Guido Westerwelle, ya ce wannan mataki da Roumaniya ta dauka ya ba shi matakukar mamaki, ta la'akari da yadda sauran kasashe 26 na EU suka bada hadin kai ga bukatar Sabiya ta ajje takaradar neman takara.

Shugaban kasar Sarbiya Boris Tadic ya ce za su cigaba da gwagwarmaya har sai sun cimma buri:Za mu ciga ba da kokowa, ba za mu yi kasa a gwiwa ba, sai mun kai tudun dafawa.

A yayin da ya ke bada hujjoji, ministan Roumaniya mai kula da al'amuran Turai, ya ce kasarsa ta yi hakan, domin cilastawa hukumomin Belgrade, su kara mutunta 'yancin 'yan Romaniya su dubu 30 da ke zaune a kasar Sabiya.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu