Takardun kudin euro sun fara daidaituwa
September 8, 2011Babban bankin Turai ya ce kuɗin ruwan da yake samu ya ɗore a kan kashi ɗaya da ɗigo biyar tun bayan da ya ƙara shi a watannin Afrilu da Yuli. Shugaban bankin Jean Claude Trichet ya ce bankin a shirye yake ya tallafawa bankunan ƙasashen da ke amfani da takardun kuɗin bai ɗaya na euro amma kuma ya yi garagaɗin cewa akwai sharuɗda masu tsauri. Shugaban bankin ya kuma soki lamirin shugaban babban jamiyyar adawar Jamus ta Social Democratic Party wato Sigmar Gabriel wanda ya kushe matakin da bankin ya ɗauka, na sayen takardun hannayen jarin gwamnati. To sai dai Trichet ya ce bankin ya riga ya yi aikinsa wajen tabbatar da daidaituwar takardun kuɗin na euro kamar yadda gwamnatocin demokraɗiyyan na kasashen turan suka buƙace shi da yi, inda ya bayyana cewa wannan ne rikicin kuɗi mafi muni wadda Nahiyar turan ta taɓa gani tun bayan yaƙin duniya na biyu.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Umaru Aliyu