Take hakkin bil'adama a Iran
December 22, 2010Babban zauren mashawartar Majalisar Ɗunkin Duniya ya yi suka da babbar murya dangane da take hakkin bil adama a ƙasar Iran. Kudurin da mashawartar ta zartar na bayyana matukar damuwa dangane da cigaban take hakkin Jama'a a wannan ƙasa.
Ƙudurin wanda ya samu amincewar wakilan ƙasasahe 78 da adawar 45, kana 59 suka ki bayyana, ya bayyanar da yadda ake zartar da hukuncin cin zarafi da mutuncin da Mutane a ɓangaren hukumomin na Iran, kama daga hukuncin bulala, azabtarwa, da yanke haɓobi.
Zauren majalisar kazalika ya lura da karuwar zartar da hukuncin kisa a Iran ta hanyar bindigewa, rataya da kuma jifa da duwatsu.
To sai dai a yau din nan ne aka zartar da hukuncin bulala 80 wa wani ɗan ƙasar ta Iran a bainar jama'a. Kampanin dillancin labarai ta ISNA ta sanar da cewar an yanke masa hukuncin ne sakamakon samun shi da laifin shan giya, wanda ke zama gargaɗi ga sauran masu irin wannan hali.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu