1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

COVID-19: Ana take hakki 'yan jarida

Koch Martin ATB/LMJ
April 21, 2020

A rahoton da ta fitar, kungiyar kare hakkin 'yan jarida ta duniya wato Reporters Without Borders, ta bayyana damuwa kan yadda wasu kasashe ke fakewa da yaki da cutar da yada labaran karya suna tauye hakkin 'yan jaridar.

https://p.dw.com/p/3bE98
Pressefreiheit Symbolbild
'Yancin 'yan jarida na cikin garariHoto: picture-alliance/dpa/O. Berg

A karo na hudu a jere rahoton ya nuna kasar Norway ita ce akan gaba yayin da kasashen Finland da Denmark ke biye mata, sai kuma kasar Koriya ta Arewa da ta kasance karshe wajen tauye wa 'yan jarida 'yancin fadin albarkacin baki, wacce ke a matsayi na 180 inda ta yi musayar matsayi da kasar Turmenistan wadda ta zama kutal a bara, yayin da kasashen Eritrea da Chaina suke a matsayi na 178 da 177.

Chaina da Saudiyya da Masar na kan gaba

Masu mulkin danniya da shugabannin kama karya suna kara kokari a fili karara, wajen danne 'yancin samar da bayanai daga kafofi masu zaman kansu ko ta halin kaka. Rahoton ya bayar da misalan kasashe kamar Chaina da Saudiyya da Masar cikin muhimman kasashe a duniya da ke tauye 'yan jarida, inda suke tsare da ma'aikatan yada labarai da dama a gidan yari saboda ayyukansu. Kamar yadda babban sakataren kungiyar 'yan jaridun ta duniya Christoph Deloire ya nunar.

Reporter ohne Grenzen: Die Welt hat Chinas Zensur zu spüren bekommen
Cin zarafin 'yan jarida a ChainaHoto: picture-alliance/dpa/AP/N. H. Guan

Haka ma dai a sauran kasashe, batun ya fito karara a 'yan watannin da suka gabata, yadda 'yancin 'yan jarida ya shiga cikin halin ha'ula'i. Annobar Coronavirus ta hadiye komai, inda ake fakewa da ita ana tauye 'yan jaridu a fadin duniya. A kasashen da aka sami ci-gaba a tsarin jadawalin, Jamus ta gusa da mataki biyu zuwa matsayi na 13 daga matsayi na 11. An sami raguwa matuka na hare-hare akan 'yan jarida kamar yadda rahoton na shekara-shekara ya nunar, idan aka kwatanta tun daga shekarar 2013. Babban dalili shi ne babu zanga-zangar masu ra'ayin rikau, idan aka kwatanta da shekarun 2019 da kuma lokacin bazara na shekarar 2018 a biranen Chemnitz da Köthen.

Fakewa da labaran karya

A 2019 kungiyar ta lisafa hare-hare akalla 13 da aka kai wa 'yan jaridu a Jamus sabanin hare-hare akalla 22 da aka gani a shekarar da ta gabata. Kungiyar 'yan jaridun ta kasa da kasa ta kuma nuna cewa a jadawalin kasashen na baya-bayan nan, kasashe da dama suna tauye 'yancin fadin albarakacin baki ta hanyar yin togaciya da labaran karya, inda kungiya ta bayar da misali da kasashen Singapore da Jamhuriyar Benin. 
A sauran kasashe kamar Rasha da Indiya da Filifin da kuma Vietnam sukan haddasa takaddama da gangan ta hanyar tsokana a kafar Internet domin samun damar haifar da rashin jituwa, wanda hakan zai ba su damar karkata akalar ra'ayin da suke so su cusa a zukatan al'umma da kuma kaskantar da ma'aikatan kafofin yada labarai.

Russland Moskau Proteste gegen Internet-Zensur
Ana sanya idanu kan masu amfani da Internet a RashaHoto: Reuter/S. Zhumatov

Babban sakataren kungiyar 'yan jaridun ta kasa da kasa Christoph Deloire ya ce sakamakon da 'yan jaridu ke gamuwa da shi da kuma hadarin da suke shiga, abin takaici ne kuma da ban tsoro yana mai cewa: "A kasashe kamar Amirka da Brazil  shugabannin da aka zaba bisa tafarkin dimukuradiyya, sune suke haddasa kiyayya da gaba domin boye gazawar manufofinsu. Irin wannan ya haifar da tarzoma akan 'yan jaridu a wurare da dama a shekarar 2019. Hatta a kasashe kamar Spain da Italiya da Girka masu tsattsaurar akidar kishin kasa da kungiyoyin 'yan ra'ayin rikau, ba sa boye barazanarsu."

Kungiyar Reporters Without Borders ta ce, idan har ana bukatar samun bayanai ba tare da shamaki ba daga kafofi masu zaman kansu musamman a irin wannan lokaci mawuyaci, to kuwa dole ne a tabbatar da sakarwa 'yan jaridu mara su gudanar da cikakken bincike.