1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takun saka tsakanin Iran da Maroko

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 2, 2018

Kasar Iran ta musanta cewa ta na taimakon 'yan gwagwarmayar Polisario da ke neman 'yancin kai daga Maroko tare da kafa kasar Saharawi mai cikakken iko.

https://p.dw.com/p/2x3Me
Iran - Hassan Rohani
Shugaban kasar Iran Hassan RohaniHoto: IRNA

Kafafen yada labaran kasar Iran din sun ruwaito kakakin ma'aikatar harkokin kasashen wajen kasar, Bahram Ghasem na bayyana zargin da Marokon ke wa Iran din da "zargin da bashi da tushe balle makama." Ya kara da cewa Iran na mutunta 'yancin kowacce kasa. Kalaman na Ghasem na zuwa ne kwana guda bayan da Marokon ta bayyana datse huldar diplomasiyya da Iran din, a abin da ministan harkokin kasashen ketare na Marokon Nasser Bourita ya bayyana da cewa kasarsa na da cikakkiyar shaida na cewa tun daga shekara ta 2016, kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanan da ke samun goyon bayan Iran din na bayar da horo da kuma tallafin kudi ga 'yan Polisario da ke fafutukar samun 'yancin kan yankin Saharawi daga kasar Maroko. Ministan ya kara da cewa a watan da ya gabata kungiyar ta Hezbollah ta aike da kashin farko na makamai ga 'yan Polisario, wanda hakan ce ma ta sanya Marokon datse dangantakar da ke tsakaninta da Iran din. Tuni dai ita ma a nata bangaren, kungiyar ta Hezbollah ta musanta wannan zargi.