1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takun saka tsakanin Nijar da Faransa

Gazali Abdou Tasawa AH
September 1, 2023

A ranar 19 ga watan Febuwarin 1977 ne Nijar ta cimma yarjejeniyar tsaro ta farko da Faransa, yarjejeniyar da ta tanadi bayar da horo ga sojojin kasar ta Nijar.

https://p.dw.com/p/4VrO9
Hoto: Sebastien Rieussec/Hans Lucas/IMAGO

Yarjejeniya ta biyu kasashen biyu sun sanya hannu kanta ne a ranar 25 ga watan Mayun 2013, wacce ta tanadi dokokin halitta girke dakarun kasar Faransa a Nijar da sunan tabbatar da tsaro a yankin Sahel baki daya. A ranar 19 ga watan Yulin wannan shekara dai ta 2013, Faransa da Nijar suka cimma yarjejeniyar da ta tsaida ‘yancin sojojin Faransa da ke zaune a Nijar da sunan yaki da matsalolin tsaro. Yarjejeniya tsaro ta hudu kasashen biyu sun sanya hannu kanta a ranar biyu ga watan Janerun shekaru ta 2015, da kuma ta tanadi izinin girke sojojin Faransa da kuma izinin gudanar da aiki a cikin kasar ta Nijar. Sai kuma ta karshe wacce kasashen biyu suka cimma a ranar 28 ga watan Aprilun 2020 wacce ta kayyade dokoki ‘yancin zaman sojojin  rundunar Takuba a Nijar da ke zama gyaran fuska ga yarjejeniyoyi biyu da kasashen biyu suka cimma a shekara ta 2013, Sai dai  akwai bambamcin wa'adin izinin soke yarjejeniyar daga wannan yarjejeniya zuwa waccan inda wata ke da wata daya wata watanni uku wata kuma watanni shida.

Wa'adin karshe na ficewar sojojin Faransa a Nijar

Burkina Faso | Französische Armee
Hoto: Michele Cattani/AFP/Getty Images

A jumulce dai yarjeniyoyi biyar ne kasashen biyu na Nijar da Faransa suka cimma a tsakaninsu tun bayan samun ‘yancin kan kasar. Kuma a lokacin da ya rage ‚yan awoyi wa‘adin farko na wata daya da aka bai wa sojojin Faransar su fice daga kasar ya cika, Yanzu haka dai kungiyoyin masu goyon bayan juyin mulki a Nijar sun sha alwashin soma zanga-zanga ranar Asabar(02-09-23) a gaban cibiyar barikin sojojin da dakarun Faransa 1500 ke girke a birnin Yamai, zanga-zangar da suka ce ba za tsaida ta ba har sai ranar da sojojin Faransar za su fice daga kasar baki daya.