Nijar: Faransa ta yi watsi da korar jakadanta
August 26, 2023Fadar gwamnatin Faransa (Quai d'Orsay) da kanta ce ta yi wannan martani da Yammacin Jumma'a (25.08.2023) jim bayan sanarwar majalisar sojin ta Nijar, inda ta ce sojojin ba su da hurumin daukar wannan mataki domin su ba halastatun jagorori ba ne.
Majalisar sojojin ta Nijar karkashin Birgediya janar Abdourahamnane Tiani ta ce ta dauki matakin korar jadadan na Faransa ne sakamakon kin amsa gayyata i zuwa taro da ministan harkokin kasashen ketare na Nijar din ya yi masa.
Karin bayani: Sabuwar baraka tsakanin Nijar da Faransa
Wannan takun saka da ke dada kamari tsakanin sabin jagorin sojan na Nijar da Faransa da ta yi wa kasar mulki mallaka na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar ECOWAS ke kara matsa lamba ga sojojin na su dawo da mulkin farar hula wanda suka kifar yau da kusan wata guda yayin da sojojin ke ci gaba da sukuwa a kan dokin na ki.
Karin bayani: ECOWAS na kan bakanta a kan Nijar