1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha na fuskantar kalubale a Bakhmout

February 16, 2023

Sojojin hayan Rasha na Wagner sun ce sakamakon yadda ake samun takun saka tsakanin kungiyar da mayan jam'an sojan Rasha kan bada umurni a filin daga zai yi wuya Rasha ta kame birnin Bakhmout na kasar Ukraine.

https://p.dw.com/p/4Nc9U
Ukraine Bachmut, Region Donezk | Rauch über der Stadt
Hoto: Yasuyoshi Chiba/AFP/Getty Images

Shugaban kungiyar Wagner Evguéni Prigojine ne ya yi wannan faruci inda ya ce ko da Rasha za ta kame birnin Bakhmout na kasar Ukraine sai an kai izuwa watan Maris ko Aprilu na wannan shekarar.

Furucin da ya yi a wani faifan bidiyo, na zuwa ne a daidai lokacin da Rasha ke matsa kaimi domin samun galaba wajen kame birnin da ke gabashin Ukraine kafin cika shekara guda da mamayar da ta kaddamar a kasar.

Mista Prigojine ya kuma kara da cewa matukar Rasha na son samun galaba sai ta dakile hanyoyin da Ukraine ke samun karin makamai daga kasashen kawancan kungiyar tsaro ta NATO.

A makonni masu zuwa ma dai kasashen Yamma na shirin kara aike wa Ukraine din karin makamai na zamani da suka hada da motoci masu sulke da tankokin yaki da kuma makaman atilare wadanda za su iya haifar wa Rasha cikas wajen cimma burinta a Ukraine.