Takunkumin Amirka da Tarayyar Turai kan Rasha
July 17, 2014Kasar Amirka da Tarayyar Turai, sun kara tsaurara matakan takunkumi kan Rasha a yammacin jiya Laraba (16.07.2014), bisa dalilan rawar da take takawa a rikicin Ukraine, inda daga nata bengare kasar Amirka ta dauki matakan da suka shafi fannin tattalin arziki kan kasar ta Rasha.
Sai dai da yake mayar da murtani a yau Alhamis, Shugaban kasar ta Rasha Vladimir Poutine, ya ce iri-irin wannan mataki da Amirka take dauka, na iya gurbatar da dangantakar da ke tsakanin Amirkar da Rasha, kuma hakan zai haifar wa Amirka manya-manyan matsaloli.
Kasar ta Amirka dai ta saka kanfanin sarrafa iskar Gaz din nan na Rosneft na kasar ta Rasha a cikin bangarorin da takunkumin ya shafa, sannan kuma wannan takunkumi zai shafi bankin Gazprom na kasar ta Rasha.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Usman Shehu Usman