1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta sake sa wa Iran takunkumi

Abdul-raheem Hassan
August 7, 2018

Matakan sun tanadi toshe wa Iran kafar hada-hadar kudi da sayar da haja a kasashen waje. Wannan ya zo ne a daidai lokacin kasar ke fama da zanga-zangar nuna damuwa kan tabarbarewar tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/32j3l
USA Donald Trump zum Atomdeal mit Iran
Hoto: Reuters/J. Ernst

Sabon takunkumin karya tattalin arziki da Amirka ta aza wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya fara aiki watanni biyu bayan da Amirka ta janye daga yarjejeniyar nukiliya ta kasa da kasa da aka cimma a shekara ta 2015.

Sai dai masu zuba jari na kasashen Turai sun soki lamirin shugaba Donald Trump, tare da bayyana aniyar ci-gaba da goyon bayan Iran da kamfanonin Turai da ke gudanar da ayyukansu a kasar. Amma kuma a daya hannun, yawancin kanfanonin sun riga sun sanar da janyewa daga kasar ta Iran.

Da y ke martani kan sabbin mataka shugaba Hassan Rouhani, ya ce matakan ba za su taimaka wa yunkurin Trump na neman sulhu ba illa kara ta'azzara tsamin dangantaka tsakaninsu.