1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jaridun Jamus: Afirka ta Kudu ta dau hankali

Suleiman Babayo LM
January 17, 2025

HAlin da masu hakar ma'adinai a Afirka ta Kudu ke ciki da siyasar Mozabique, na cikin abubuwan da suka dauki hankalin Jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/4pGJ5
Afirka ta Kudu I Hakar Ma'adinai | Haramtacciyar Hanya
Masu hakar ma'adinai ta haramtacciyar hanya na halaka a Afirka ta KuduHoto: Kim Ludbrook/dpa/picture alliance

Jaridar die Tageszeitung ta yi sharhinta ne kan halin da masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba ke ciki a Afirka ta Kudu, inda ta nunar da cewa mutuwar baki 'yan kasashen ketere masu hakar ma'adanan na da dangantaka da tarihin kasar na nuna wariyar launin fata. Jaridar ta bayyana cewa hakar ma'adanai musamman zinare na taka rawa kan tattalin arzikin kasar, inda a shekarun 1970 da 1980 matasa daga kasashe irin Lesotho da Botswana da Mozambik suke samun kudin shiga.

Shi kansa birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu ya samo asali daga zinare, kuma zinariyar ta taka rawa sosai wajen wajen gina tattalin arzikin kasar. Kawo yanzu masu hakar ma'adanan ba bisa ka'ida ba kimanin 246 suka tsira daga kawanyen da 'yan sandan Afirka ta Kudu suka yi a wajen, yayin da mutane 78 suka halaka. Wannan na zuwa ne bayan da aka da aikin ceton mutanen da suka makale a ramukan tonan ma'adanan ba bisa ka'ida ba sakamakon killace yankin da jami'an tsaro suka yi tsawon watannin.

Mosambik Maputo 2025 | Präsident Daniel Chapo bei interreligiösem Versöhnungsgottesdienst
Sabon shugaban Mozambique Daniel Chapo ya dare madafun ikoHoto: Nádia Issufo/DW

Sai kuma jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung da ta ce an rantsar da Daniel Chapo a matsayin sabon shugaban kasar Mozambique, yayin da birnin Maputo fadar gwamnatin kasar ya kasance shiru saboda matakan da jami'an tsaro suka dauka. An yi bikin ba tare da 'yan kallo ba, saboda rikicin siyasar da kasar take ciki. Babban dan takara na bangaren adawa Venâncio Mondlane ya yi watsi da sakamakon zaben, abin da ya janyo zanga-zangar da ta yi sanadiyar mutawar mutane da dama.

Rahotanni sun nuna cewa shugabannin kasashe biyu kacal suka halarcin bikin rantsar da sabon shugaban kasar na Mozambik, wato Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu da Shugaba Umaro Sissoco Embaló na Guinea-Bissau. Akwai wasu mataimakan shugaban kasa da ministoci daga kasashen Afirka. Ita ma Potugal da ta yi mulkin mallaka a kasar, ta tura minista. Shi dai Daniel Chapo ya karbi madafun ikon kasar ta Mozambique ne, daga hannun tsohon Shugaba Filipe Nyusi wanda ya kammala wa'adin mulkinsa na shekaru 10, inda aka zabe shi shekaru biyar sau biyu kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Libiya | Yakin Basasa | Khalifa Haftar | Rasha | Yunus-bek Yevkurov | Sojoji
Ministan tsaron Rasha Yunus-bek Yevkurov yayin ziyararsa ga Khalifa Haftar a 2023Hoto: Media office of Khalifa Haftar/AFP

A nata sharhin mai taken daga kasar Libiya yanzu Rasha tana iya shiga lamuran kasashen Afirka, jaridar Neue Zürcher Zeitung ta nunar da cewa masanin tsaro Hager Ali ya ce mahukuntan birnin Moscow suna iya jibge dakaru kudancin Turai gina rundunar soja a yankin arewacin Afirka. An kwashe shekaru, Rasha tana horas da dakarun Siriya karkashin tsohon shugaban kasar Bashar al-Assad hada jirage masu sarrafa kansu. Tun bayan rushewar gwamnatin Assad a watan Disambar bara dakarun na Rasha suna komawa kasar Libiya, inda suka ya da zango a birnin Benghazi na arewacin Libiya.

Sudan | Mohamed Hamdan Daglo | RSF
Jagoran mayakan RSF na Sudan, Mohamed Hamdan DagloHoto: Ashraf Shazly/AFP

Takunkumi a karshe, da wannan kalaman jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi sharhi kan matakin Shugaba Joe Biden na Amurka mai barin gado kan takunkumin da gwamnatinsa ta kakaba wa mayakan RSF na Sudan. Amurka ta dauki matakin kakaba musu takunkumin ne, saboda yadda suke ci gaba da aikata laifun yaki tun lokacin da yaki ya barke tsakanin mayakan RSF din da sojojin gwamnati. Tunkunkumin ya shafi jagoran mayakan na RSF, Mohamed Hamdan Daglo da ake zargi da aikata kisan kare-dangi a rikicin na Sudan.