1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Taliban ta aikata ta'addi

Abdourahamane Hassane
August 2, 2021

Jakadojin Amirka da Birtaniya a birnin Kabul na Afghanistan sun zargi 'yan Taliban da aikata kisan kiyasu a kan farar hula a kudanci Afghnaistan.

https://p.dw.com/p/3yRcV
Afghanistan Konflikt Taliban Terrorismus
Hoto: HOSHANG HASHIMI/AFP via Getty Images

Jami'an diplomasiyar sun ce 'yan Taliban wadanda suka karbi iko da yankin Spin Boldak a cikin watan Yuli da ya gabata sun fatattaki jama'ar yanki a matsayin ramuwar gayya. A cikin sanarwa da suka bayyana ta hadin gwiwa ta nuna cewar 'yan Taliban din sun kashe farar guda 40 wadanda ba mayaka ba ne a yankin  spin Boldak galibi ma'aikatan gwamnati.