Taliban na bikin cika shekaru biyu a mulki
August 15, 2023Gwamnatin Taliban ta gudanar da bikin cika shekaru biyu da karbe mulki a Afganistan tare da mayar da kasar karkashin tsauraran dokokin Islama, matakin da kasashe da dama na duniya ke suka. Tutocin kasar sun ta kadawa a shingayen binciken na Kabul babban birnin kasar, domin tunawa da ranar da gwamnatin da ke samun goyon bayan kasashen yammacin duniya ta fadi tare da maye gurbinta da ta 'yan Taliban.
Sanarwar da hukumomin Afghanistan suka fitar ta bayyana ranar 15 ga watan Agustan shekarar 2021 a matsayin ranar nasara da ta share fagen kafa gwamnatin Musulunci a kasar. Sanarwar ta kara de cewa, kwace birnin Kabul shekaru biyu da suka gabata ya nuna cewa babu wata kasa ta ketare da za ta iya sake yi wa Afghanistan katsalandan.
Ita dai gwamnatin Taliban ta dauki tsauraran matakan addinin Musulunci musamman a kan mata tun bayan da ta hau kan karagar mulki, matakin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin nuna wariyar jinsi.