Taliban ta bukaci zuwa taron majalisar Dinkin Duniya
September 22, 2021A cikin wasikar da ya aikawa hedikwatar majalisar, ministan harkokin waje na gwamnatin Taliban Amir Khan Muttaqi ya bukaci a bai wa kasar damar gabatar da jawabi a taron kolin karo na 76 da yake gudana a birnin New York na kasar Amirka.
A wasikar, mayakan Taliban sun bukaci yin wasu sauye-sauye na jakadun kasar, inda ta ce ta na son maye guraben wakilan Afghanistan na hambararriyar gwamnati a Majalisar da suka hada da Suhail Shaheen da kuma Ghulam Isaczai.
Tuni dai kakakin Majalisar Farhan Haq ya ce an aika da wasikar ga kwamittin da ke duba takardu, wanda shi ne ke da alhakin baiyana shugabanni da kuma wakilan kasashen da aka amince da su a Majalisar.
Tun bayan janyewar dakarun kawance na NATO da kuma Amirka, Taliban ta sami cikakken iko a Afghanistan; ta kuma sake kafa masarautar musulumci bayan shekaru 20. Sai dai har kawo yanzu ba a amince da gwamnatinta a matsayin halattaciya ba.