Taliban sun karbe wani yanki a Afghanistan
March 1, 2017Talla
'Yan Kungiyar ta'adda ta Taliban sun karbe wani yanki a Afghanistan kamar yadda wani mazaunin arewa maso gabashin garin Baglan kusa da in da yan ta'addan suka yi sansani ya shaida wa manema labarai.An wayi gari da tashin bama-bamai abin da yayi sanadiyyar rasa rayuka da dama wanda suka hada da mata da kananan yara bayan yan ta'addan sun tsare duk wata kofa da mutane za su iya tserewa kamar yadda kakakin kungiyar 'ta'addan ta Taliban ya rubuta a shafin Twitter cewar a halin yanzu suna tsare da jami'an tsaro goma sha uku sannan sun harbe mutum uku. Yankin Baglan ya dade yana fama da irin wannan farmaki na 'yan Taliban a afghanistan.